Wani Gwamna Ya Samo Sabbin Kudi Na N500m Yayin Talaka Ke Neman Na Koko, Inji El-Rufai
- Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da shan wahala game da sabbin kudi, gwamna El-Rufai ya bude batutuwa
- Ya ce akwai gwamnan da ya samo sabbin Naira da suka kai na N500m, kuma a hakan an yi sauyi don ‘yan siyasa
- Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ‘yan siyasa ke da bankuna, sauyin kudi da boye su ba zai yi tasiri a kansu ba
Najeriya - Wani gwamnan da ba a bayyana sunansa ba ya samo N500m na sabbin Naira da ke ba ‘yan Najeriya wahalar samu daga wani banki, inji gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.
Malam ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da kafar labarai ta BBC Hausa, inda yake bayyana kokensa game da batun sauyin kudi da wa’adin daina amfani da tsoffi.
A cewarsa, ‘yan siyasan da aka yi sauyin kudi tare da sanya wa’adin mayar da tsoffi domin su tuni sun fara mallakar kudaden ta hanyar da suke da ita.
A tun farko, gwamnatin Najeriya ta buga sabbin N200, N500 da N1000 tare da bayyana wa’adin daina amfani da tsoffinsu, lamarin da ya jawo cece-kuce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba laifi bane sauya kudi, amma...
Da yake tsokaci game da sauyin, Malam Nasiru ya ce sam ba laifi bane don gwamnati ta sauya kudi, saboda kasashen duniya na yin hakan.
Hakazalika, ya amince hakan zai iya kawo ci gaba ga kasar, amma ya kamata a duba wasu abubuwa kafin fara kawo batun sauya kudin Najeriya.
A fahimtarsa, dago maganar sauya kudi tare da sanya matsattsen wa’adi zai jawo matsala ga siyasa da tattalin arzikin kasar nan.
Kan talaka zai kare, ‘yan siyasa su ke da banki
Don haka, gwamnan yace wannan wahalar duk a kan talaka za ta kare, domin wasu ‘yan siyasan suna da bankuna na kansu a kasar.
Daga nan, gwamnan ya ambaci cewa, wani gwamna daga cikin gwamnonin kasar nan ya samo sabbin Naira da suka kai N500m.
Saboda haka, yace kamar kwalliya bata biya kudin sabulu ba, domin wadanda aka yi abin don su basu shan wahalar da talaka ke sha.
Ya kuma ce, ya kamata shugaban kasa ya duba, domin shi da sauran gwamnonin APC basu amince da wa’adin da aka saka ba, don haka a daga zuwa watanni.
Za a daina amfani da tsoffin takardun Naira a ranar 10 ga watan Fabrairun 2023, kamar yadda CBN ya bayyana.
Kwankwaso ya ce sauyin kudi talaka ne zai sha wahala
Ba El-Rufai kadai ba, tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa a NNPP, Rabiu Kwankwaso ya fadi magana irin wannan.
Ya ce ‘yan siyasan da aka yi wannan sauyin kudi domin su suna da bankuna, don haka samun kudi ba zai ba su wahala ba.
Ya zuwa yanzu dai talakawan Najeriya na ci gaba da tikar layi a bankuna da ATM har da kokuwa domin cire sabbi ko tsoffin kudi saboda harkokin yau da kullum.
Asali: Legit.ng