Attijirin Najeriya Da Yake Son Siyan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Ingila Sheffield United Kan Biliyan N50.6bn

Attijirin Najeriya Da Yake Son Siyan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Ingila Sheffield United Kan Biliyan N50.6bn

  • Wani mashahurin attajirin dan Najeriya yana kokarin mallakar tawagar kwallon kafa a Ingila
  • Dozy Mmobuosi ya shiga tattaunawa da Sheffield United don mallakar kungiyar kan kudi N50.6
  • Mmobuosi dan kasuwa ne masanin kimiyya da ya kirkiri Tingo Mobile, kamfanin hada wayoyi a Najeriya

Wani babban dan kasuwar fasaha, Dozy Mmobuosi na daf da mallakar Sheffield United, wata kungiya kwallon kafa a kasar Ingila kan kudi fam miliyan 90 saboda matsalolin cinikayyar yan wasa a tawagar.

Rahotanni sun bayyana cewa Mmobuosi yana matakin karshe don kammala cinikin. An bayyana yana jiran sahalewar mammalakan kungiyoyin firimiya, amma banda wannan, ya kammala komai.

Dozy Mmobuosi
Attijirin Najeriya Da Yake Son Siyan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Ingila Sheffield United Kan Biliyan N50.6bn. Hoto: Mmobuosi
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mmobuosi ya kirkiri kamfanin Tingo mobile a Najeriya a shekarar 2001, wanda kamfanin ya cigaba da bunkasa tun daga wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Toh fa: CBN na kuntatawa talakawa da sunan hukunta 'yan rashawa, inji sanata Shehu Sani

Ya kirkiri wata gidauniya a shekarar 2021 wanda yake bajakolin cigaban Afrika ga duniya yadda yan Afrika za su samu kima.

Mmobuosi ya shahara matuka wajen tallafawa da kuma cigaban ilimi, lafiya da kuma kimiyyar sadarwa a Najeriya.

Tingo Mobile a yanzu haka na da kimar da ta haura fam biliyan 7.

Abubuwan da ya kamata a sani game da Mmobuosi

Ya kammala digirinsa na farko a bangaren kimiyyar siyasa daga jami'ar Ambrose Ali University kuma shine ya fara kaddamar da harkar banki ta gajeran sakon waya (SMS banking) da aka fi sani da Flashmecash, wanda bankin FCMB ke amfani da shi, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya bayyana.

Mai bada shawara ne shi a manyan kungiyoyi da masana'antu kuma yana da digiri a fannin cigaban birane daga jami'ar Universiti Putra a Malaysia.

Sannan, Mmobuosi ya kammala karatu a bangaren gudanarwa da kuma shugabanci a wata tsangayar koyon kasuwanci a Oxford, a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Hukumar yan sanda ta yi magana game da mutumin da ya mutu a layi ciki banki

Ya bude kamfanin harhada wayoyin hannu guda biyu a Najeriya don taimaka yan Najeriya samun damar amfani da yanar gizo da kuma wayoyin zamani.

Attajirin Kano AbdulSamad Ya Zama Na 4 Cikin Jerin Masu Kudi A Afirka

A wani rahoton, Alhaji AbdulSamad Rabiu ya zama mutum na hudu mafi yawan dukiya a nahiyar Afirka, bayan ya doke attajirin kasar Masar, Nassef Sawarus yan watanni bayan ya zama na biyu a Najeriya.

A kwanakin baya, kun ji yadda AbduSamad ya kara samun daukaka ya zama na biyu a Najeriya bayan Aliko Dangote, bayan wuce Mike Adenuga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel