CBN Ya Biye Sabbin Kudi Ya Bar Mutane Cikin Wahala, Badaru

CBN Ya Biye Sabbin Kudi Ya Bar Mutane Cikin Wahala, Badaru

  • Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, ya koka kan yadda talakawansa ke wahala wajen neman sabbin takardun naira
  • Badaru ta bakin ɗaya daga cikin kwamishinoninsa ya ce mazauna Jigawa sun shiga kakanikayi sanadin ƙarancin naira
  • A cewarsa a binciken da ya gudanar ya gano cewa CBN bata baiwa bankuna isassun kudin da zasu sanya a ATM

Jigawa - Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda babban bankin kasa CBN ya gaza samarwa mutane sabbin takardun kuɗi.

Tribune tace Gwamnan ya nuna damuwarsa game da karancin sabbin kuɗin ta bakin kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki na jihar, Babangida Umar Gantsa.

Gwamna Badaru Abubakar.
CBN Ya Biye Sabbin Kudi Ya Bar Mutane Cikin Wahala, Badaru Hoto: punchng
Asali: Facebook

A cewarsa, "Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammed Badaru Abubakar ya shiga damuwa matuka game da yadda CBN ya jefa al'umma cikin wahala."

"CBN ya jefa mutane cikin kakaniyi kan sauya takardun naira da kuma gaza wa wurin wadata bankunan kasuwanci da tsabar sabon kuɗin."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hadimar Gwamna Tambuwal Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Badaru ya ƙara da bayanin cewa mutanen Jigawa sun shiga yanayin wahala sakamakon tangal-tangal ɗin harkokin tattalin arziki da walwala saboda rashin takardun kuɗi a hannu.

Punch ta ruwaito Kwamishinan na cewa:

"Kuna gani da kanku mutane na kwana a layin ATM domin su cire kuɗi daga Asusun bankunansu. Damuwa da hakan gwamna ya umarci na zagaya bankuna na gano halin da ake ciki."
"Manajoji sun tabbatar mun da cewa CBN ya ƙi sakar masu isassun kuɗin da zasu sanya a ATM mutane su samu damar cirewa. Akwai ATM ɗin da na kirga mutane 250 a layi."
"A wasu bankunan kuma zaka samu mutane sama da 250 suna jiran a sa kuɗi a ATM, sun faɗa mun da yawansu nan suka kwana."

Kwamishinan ya ƙara da cewa tuni wannan matsalar ta durƙusad da kasuwancin masu POS sakamakon rashin isassun sabbin takardun kuɗin.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Gwamnan CBN Ya Tona Asiri Kan Sabbin Kudi, Ya Faɗi Babban Laifin Bankuna

CBN Ya Shigo da Bankunan Microfinance da Masu POS a Zamfara

A wani labarin kuma CBN Ya Ƙara Shigo da Abu 2 da Zasu Rage Wa 'Yan Arewa Wahalar Neman Sabbin Kuɗi

Kwanturolan babban bankin na jihar, Abbas Buhari, ya ce sun shigo da bankunan Microfinance da masu POS cikin tsarin musaya a yankunan da babu zaman lafiya.

Kwanturolan ya jaddada cewa mafi yawan kuɗin da kowane mutum zai iya musanya wa ya ba da tsoffi a ba shi sabbin naira shi ne N10,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel