‘Okowa Maciyi Amana Ne’, Shugaban Kabilar Ijaw Edwin Clark Ya Caccaki Abokin Takarar Atiku
- Abokin takarar Atiku ya sha tofin ala-tsine daga bakin shugaban kabilar Ijaw a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
- Edwin Clark ya zargi gwamna Ifeanyi Okowa da lamushe wasu kudaden da aka bayar na jihar a kwanakin baya
- Hakazalika, ya ce gwamnan ya yaudari abokansa na yankin Kudu, an nemi ya durkusa ya nemi gafararsu
Kudancin Najeriya - Shugaban kungiyar kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark ya danganta gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP da mayaudari, The Nation ta ruwaito.
Clark ya kuma nemi Okowa da ya ajiye batun takara a gefen Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasan PDP tare da neman gafarar abokansa na yankin Kudu maso Gabas a Najeriya.
Wannan shugaba na yankin Kudu masu Gabas ya dago batun ne yayin ya saura kwanaki kasa da 23 ga babban zaben shugaban kasa na 2023 a kasar.
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yanzu nake fahimtar dalilin da yasa da gangan kuma cikin rashin da’a ka yaudari abokanka na Kudu maso Gabashin Najeriya da mutanen yankin bisa burin son zuciyarka cikin tsanaki ta hanyar amince ka yi takara a gefen Alhaji Atiku Abubakar.
“Sam, da yardar Allah addu’arka ba za karbu ba. Watakila, ka manta girman laifin da ka aikata ga mutanen Kudu maso Gabashin Najeriya."
Okowa ya lamushe wasu kudaden jiharsa, inji Clark
Shugaban na kabilar Ijaw ya kuma bukaci gwamna Okowa da ya ba bahasin yadda ya kashe kudade N250bn na bashin da jihohi masu arzikin man fetur ke bin gwamnatin tarayya da aka biya jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma zargi gwamnan da yin amfani da kudaden jihar wajen gina kauyensu da sunan kashe kudi ga yankin da ke da arzikin man fetur.
Ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP da wasu manyan Kudu maso Gabashin Najeriya.
An hana Atiku filin kamfen a jihar Ribas
A wani labarin kuma, gwamnan PDP Nyesom Wike ya hana a yi amfani da filin wasa don yin gangamin kamfen Atiku a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan da a baya ya amince a yi amfani da filin, duk da cewa ya ce ba zai yiwa Atiku kamfen ba.
A sabuwar wasikar da aka gani, gwamna ya bayyana dalilan da suka ba zai bari a yi kamfen ba filin wasa.
Asali: Legit.ng