Amarya Ta Fasa Aure Kwana 1 Kafin Bikinta Bayan Ta Gano Angon Na Cikin Bashi Dumu-dumu

Amarya Ta Fasa Aure Kwana 1 Kafin Bikinta Bayan Ta Gano Angon Na Cikin Bashi Dumu-dumu

  • Wata matashiya yar Najeriya ta soke aurenta bayan ta gano cewa mai shirin zama mijinta na cikin bashi dumu-dumu
  • Matashiyar ta ci karo da masoyinta yana karbar wasika daga wata budurwa da bata taba gani ba a gidansa
  • Bayan ta binciki wasikar, budurwar ta gano cewa masoyin nata na nan da bashi jibge a kansa

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta soke aurenta kwana daya kafin bikin bayan ta gano cewa akwai wata gaskiya da mijin nata ke boye mata.

Matashiyar bata san cewa mijinta na cikin bashi ba har sai da wata budurwa ta kawo ziyara.

Matashi da wasika
Amarya Ta Fasa Aure Kwanaki Kafin Bikinta Bayan Ta Gano Angon Na Cikin Bashi Dumu-dumu Hoto: @Dominique Bell, EyeEm/Getty images
Asali: Getty Images

Ango ya boye wa amarya batun bashin da banki ke binsa

Budurwar ta mika masa wata wasika wanda ya yi saurin boyewa don kada amaryarsa ta gani, bai san cewa tana nan a kusa ba.

Kara karanta wannan

Ba Na Goge Hakorana a Ranar Lahadi: Kyakkyawar Baturiya Ta Baje Kolin Hakoranta a Bidiyo, Mutane Sun Yi Martani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin zullumi mai shirin zama amaryar ta binciki wasikar sannan ta gano cewa yana cikin bashi kuma banki na shirin kwace kadarorinsa.

Dexterouz11 wanda ya wallafa labarin a shafinta na Twitter ta ce:

"Kawar makwabciyata ta fasa aurenta ana jajiberin aurensu bayan ta gano cewa mutumin na da boyeyyen bashi da ka iya talauta iyali. Bai fada mata ba.
"Ana gobe aurensu, wata mata ka kawo ziyara sannan ta ganta tana baiwa mijinta wata wasika. Ya boye mata wasikar amma ta binciko shi cikin zullumi saboda ta zata wasikar soyayya ce.
"Ta gano cewa matar ma'aikaciyar baki cewa kuma wasika ce ta karbe kadarorinsa tunda ya kasa biyan banki bashin da take binsa. Ta ce bata auren kuma."

Kalli wallafar a kasa:

Uban amarya ya gwangwaje ango da sabuwar mota fil a leda

A wani labarin kuma, Allah ya tarbawa garin wani ango nono a kasar Zambiya inda ya samu babban kyauta na kece raini daga uban amaryarsa a ranar bikinsu.

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Yara Uku Kowane Mahaifinsa Daban Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Tace Aure Take So

Baban yarinyar wanda ya kasance attajirin dan kasuwa kuma mai taimakon al'umma a kasar Zambiya, ya baiwa surukin nasa kyautar sabuwar mota fil a leda kirar Land Rover don nuna godiya a kan son diyarsa da ya yi sannan ya zabe ta cikin mata da yawa.

Jama'a sun taya wannan ango murna inda suka shawarce shi da ya rike amaryarsa da amana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel