Yadda Mijina ya kore ni, Ya Auri Babbar Yayata: Mahaifiyar Yara 5 ta Bada Labarinta

Yadda Mijina ya kore ni, Ya Auri Babbar Yayata: Mahaifiyar Yara 5 ta Bada Labarinta

  • Wata uwa cike da alhini ta labarta yadda 'yar uwarta da suka fito cike daya ta kwace ma ta miji yayin da aka kwantar da ita a gadon asibiti
  • Uwineza Ange ta bayyana yadda bayan dawowarta daga asibiti bayan watanni biyu, ta gano yadda mijin nata ya yi watsi da yaranta biyar
  • Matar 'yar kasar Rwanda ta samu shagube daga mahaifiyarta kan yadda mijinta ke soyayya da 'yar uwarta duk lokacin da ta kai ma ta ziyara, inda ta tabbatar da abun da ta ke tsoro

Wata mahaifiyar 'ya'ya biyar ta bayyana daya daga cikin abubuwan da suka dagula ma ta lissafi a rayuwarta na yadda yayarta ke soyayya da mijinta.

Matar 'yar kasar Rwanda da ke da 'ya'ya biyar, Uwineza Ange ta fashe da kuka yayin zayyana yadda 'yar uwarta da mijinta suka ci amanarta.

Kara karanta wannan

Saurayin Ya Bar Ni Saboda Ina Kama da Gardi: Budurwa Ta Bayyana Canzawar da Tayi a Bidiyo

Mahaifiyar yara 5
Yadda Mijina ya kore ni, Ya Auri Babbar Yayata: Mahaifiyar Yara 5 ta Bada Labarinta. Hoto daga Afrimax
Asali: UGC

Uwineza Ange wacce bata taba fuskantar kwanciyar hankali a rayuwarta ba, ta ce 'yar uwarta ce tushen matsalolinta.

"Lokacin da na ke karamar, ta na musguna min ta hanyar bautar da ni kamar 'yar aikin gida. Ta haramta min dadin ilimi ta hanyar takura min da ayyukan gida marasa karewa hakan yasa nake barin aikin makaranta. Ina kula da 'ya'yanta."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Matar 'yar kasar Rwanda ta labartawa Afrimax harshen Turanci.

Ta tuna wata rana da bata da lafiya, inda aka kwantar da ita asibiti na tsawon watanni biyu.

A wannan lokacin, yayarta da mijinta ko leke basu tako asibitin duba lafiyarta ba. Hakan ya matukar damunta saboda yadda suka nuna ma ta halin ko in kula da jefata a kadaici.

"Yayin da na koma gida daga asibiti, na matukar shan mamakin gano yadda miji na ya yi watsi da 'ya'yanmu, inda ya koma rayuwa da yayata. Hakan ya kashe min jiki. Duk lokacin da nayi kokarin kiransa, ba ya daukar kiraye-kirayena."

Kara karanta wannan

Soyayya Gamon Jini: Dirarriyar Matar Aure ta Bayyana Wadan Mijinta a Bidiyo, Tace Suna Cikin Farin Ciki

- A cewarta.

Wata rana mahaifiyar Ange ta kira yayarta bayan gano bata ziyarci kanwarta yayin da ta ke asibiti ba. Sai dai mutumin ne ya dauki kiran, wanda hakan ya kara janyo zargin da ta ke game da yayar Ange da masoyin Ange.

Mahaifiyar Ange ta zayyana wa 'diyarta komai game da lamarin. Hakan ya sa Ange ta yanke shawarar zuwa don ganin ma idonta.

"Lokacin da muka shiga falon, mun iske su su na wani babban tari, suna shan giya gami da holewarsu."

- A cewarta.

Ange ta dawo gida da sauran mijin zau biyo su ganin yadda suka kamasu dumu-dumu, amma bau yi hakan ba.

Mijin nagari: Matar aure ta samu kyautar adaidaita sahu daga mijinta

A wani labari na daban, wani magidanci ya Gwangwaje matarsa da kyautar adaidaita sahu biyu ranar bazday din ta.

Ya hada mata da waya tare da fulawa inda ta fashe da kukan dadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel