Jerin Jihohi 6 da ke Gaba Wajen Cin Bashi da Jihohi Mafi Karancin Bashi a Kan Su
- Gwamnatin Tarayya ta karbo aron Naira Tiriliyan 42 a gida da waje, bashinta ya karu da 2.85% a 2022
- A ‘yan watanni bashin da ake bin Gwamnati ya tashi, kenan an aro Naira Tiriliyan 4 a watanni uku
- A jerin Jihohin da ake bi tulin bashi a Kasar nan, Legas a kan gaba, Kebbi ke da mafi karancin bashi
Abuja - Bashin da ake bin Najeriya zuwa karshen shekarar 2022 ya karu da 2.85% idan aka kamanta da adadin bashin da ke kan kasar watanni uku baya.
Wani rahoto da Leadership ta fitar ya ce har zuwa karshen watan Yuli na 2022, kudin da ake bin Gwamnatin Najeriya bashi shi ne N42.84tr (watau $101.9bn).
Amma a watanni uku, zuwa karshen Satumban shekarar bara, bashin ya karu zuwa N44.06tr. Idan aka raba kudin ga adadin 'yan kasa, za a samu N260, 000.
An samu wadannan bayanai daga alkaluman da suka fito daga hukumar NBS a kan bashin da ke kan wuyan gwamnatin tarayya, jihohi 36 da birnin Abuja.
Rahoton da aka fitar a makon nan ya nuna gwamnatin Najeriya ta ci bashin N17.14tr (ko $39.66bn) daga kasashen waje, sannan an karbo N26.91tr a bankunan gida.
.38.91% na aron da Najeriya take yi daga ketare ne, a nan gida aka ci bashin 61.08%.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bashin da ake bin Jihohi
Idan aka yi la’akari da bashin da ake bin jihohi, hukumar NBS ta ce Legas da ake bi N877bn ce a gaba, sai Delta da Ogun su na bi mata da N272bn da N241bn.
Jihohin da ke da karancin bashi a kan su sun fito daga Arewa maso yamma, su ne Jigawa mai N44bn, sai Kebbi da ake bi N60bn sannan Katsina da N62bn.
Masu bashi sosai
1. Legas - N877.03bn
2. Delta - N272.61bn
3. Ogun - N241.78bn
Masu karancin bashi
1. Jigawa - N44.40bn
2. Kebbi – N60.13bn
3. Katsina - N62.37bn
Sanatoci na binciken kudi
Ku na da labari cewa tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, an ba Ma’aikatar sadarwa da tattalin zamani Naira Biliyan 13.9bn domin yin wasu ayyuka.
Amma Ma’aikatar tarayyar ta gaza yi wa Kwamitin majalisar dattawa cikakken bayanin inda kudin da Akanta Janar ya aika mata suka shiga.
Asali: Legit.ng