Wani Mutum Ya Yi Wa Dan Gudun Hijira Yankan Rago Kan Zarginsa Da Maita a Jihar Borno
- Wani bawan Allah ya rasa ransa sakamakon kisan gilla da wani makwabcinsa ya yi masa a sansanin yan gudun hijira da ke karamar hukumar Konduga, jihar Borno
- Wani mutum ya yi wa dan gudun hijira yankar rago a sansanin Mandarari kan zarginsa da ake da maita
- Maharan ya fara doke shi ya kar shi kasa kafin caccaka masa wuka bisa zaginsa da kashe masa mata da sauran mazauna sansanin
Borno - Wani mutum mai shekaru 40 ya yi wa wani dan gudun hijira yankar rago kan zarginsa da maita a sansanin yan gudun hijira da ke Mandarari a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, Zagazola Makama ya rahoto.
An tattaro cewa maharin ya kutsa kai cikin masaukin mamacin da misalin karfe 4:00 na yamma, ya doke shi da karfi kafin ya caccaka masa wuka sau da dama a wuyansa.
Hikima: Matashi Ya Huta Da Wulakancin Kafinta, Ya Gina Gadon Kasa Da Bulo, Hotunan Ya Girgiza Jama'a
Zagazola Makama ya fahimci cewa a lokacin da wanda lamarin ya cika da shi ya shiga wani yanayi, sai maharin ya mikar da shi a kasa sannan ya yi masa yankar rago, inda ya mutu nan take.
An yanka mutumin da ake zargi da kashe yan gudun hijira da saka masu rashin lafiya
Yan gudun hijiran sun zarge shi da aikata maita kuma cewa saboda da shi ne mutane da dama a sansanin ke kamuwa da rashin lafiya ko mutuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shaidu sun bayyana cewa ana zargin mamacin ne ya yi sanadiyar mutuwar matar mutumin da ya farmake shi.
A halin da ake ciki, wani mutum ya kuma farmakar wani dan gudun hijira da wuka a sansanin na Mandarari da misalin karfe 6:00 na yamma.
Sai dai har yanzu ba a san dalilinsa na kar harin ba amma dai an gaggauta kwasar wanda aka farmaka zuwa asibiti.
Sojoji sun yi ram da masu kaiwa mayakan ISWAP kayayyaki har su 13
A wani labari na daban, dakarun rundunar sojin Operation Hadin Kai sun yi nasarar cika hannu da wasu da ake zargin masu kaiwa mayakan kungiyar ta'addanci na ISWAP ne a jihar Borno.
Dakarun sojojin da taimakon yan sa-kai na CJTF sun kai samame kasuwar Benishiek a kokarinsu na toshe duk wata kafar samun kayayyaki ga yan ta'addan inda a nan ne suka kama matasan su 13.
Yankin na daya daga cikin manyan wuraren da yan kungiyar ta'addancin ke samun kayayyakinsu kama daga abinci, sutturu, man fetur, da dai sauran abubuwan amfaninsu.
Asali: Legit.ng