Magidanci Garzaya Kotu, Ya Nemi a Raba Aurensa Saboda matar Bata Masa Biyayya

Magidanci Garzaya Kotu, Ya Nemi a Raba Aurensa Saboda matar Bata Masa Biyayya

  • Wani mutumi ya nemi Kotun yanki a Ilorin, babban birnin jihar Kwara ta raba aurensa saboda matar bata jin maganarsa
  • Lauyan wacce ake kara yace matar da yake wa aiki ta amince da raba auren amma ba kan tuhumar da ake mata ba
  • Bayan sauraron kowane ɓangare, Alkalin Kotun ya ɗage zaman zuwa ranar 20 ga watan Maris, 2023

Kwara - Wani magidanci, Taiwo Ajadi, ya kai karar matarsa mai suna, Mariam, gaban Kotun yanki mai zama a Ilorin kan zargin rashin ɗa'a da rashin ladabi.

Jaridar punch ta tattaro cewa Mijin ya kuma roki Kotun ta bar masa ɗawainiyar yaran da suka haifa guda uku; mace yar shekara 11, Kaninta namiji mai shekara 8 da ƙaramarsu mace mai shekaru 4.

Kotu a Ilorin.
Magidanci Garzaya Kotu, Ya Nemi a Raba Aurensa Saboda matar Bata Masa Biyayya Hoto: punchng
Asali: Twitter

Shin wacce ake kara ta amince da laifinta?

Lauyan wacce ake ƙara, Mista Maruf Ibrahim, ya shaida wa Kotun cewa wacce yake wa aiki ta amince a raba auren amma ba kan tuhumar da mijin ke mata ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Harbe Babban Ɗan Sanda Har Lahira Arewacin Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ibrahim ya bayyana wa Alkali cewa ko kaɗan Mariam ba mace bace mara biyayya ga uban 'ya'yanta kuma ko kaɗan bata da halin rashin kunya ko rashin jin magana.

Haka zalika ya ƙara da cewa matar ta nemi Kotu ta bar mata aikin kula da 'ya'yansu guda uku da Allah ya albarkace su da samu a zaman auren.

Lauyan ya bayyana yaran da ƙanana waɗanda basu mallaki hankalinsu ba kuma ya kamata Magidanci ya ɗauki nauyin biya masu kuɗin makaranta da harkokin yau da kullum.

Wane mataki Kotun ta ɗauka?

Alkalin Kotun a jihar Kwara, AbdulQadir Ibrahim, ya bukaci mai shigar da ƙara ya kawo hujjojin da ya sa ya nemi a ba shi ikon kula da ƙananan yaran uku.

Daga nan Alkalin ya ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 20 ga watan Maris, 2023, kamar yadda hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Gwamnan CBN Ya Tona Asiri Kan Sabbin Kudi, Ya Faɗi Babban Laifin Bankuna

A wani labarin kuma Kotu ta Umarci Budurwa ta Biya Saurayi N1m Bayan Karbe Masa Kudade kuma ta ki Aurensa

Wata kotu a ƙasar Uganda ta umarci wata mata a yankin Kanungu da ta biya tsohon sauranyinta sama da N1 miliyan a matsayin diyyar fasa aurensa da ta yi.

Tsoffin masoyan biyu, Richard Timwine da Fortunate Kyarikunda sun fada kogin soyayya a 2015, har suka kai ga alkawarin aure a 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262