Matashiya Ta Adana Takardun Tsoffin Kudi Saboda Tarihi, Hotunan Sun Haddasa Cece-Kuce

Matashiya Ta Adana Takardun Tsoffin Kudi Saboda Tarihi, Hotunan Sun Haddasa Cece-Kuce

  • Wata matashiya yar Najeriya ta yada hotunan tsoffin kudi da za ta ajiye saboda tarihi kuma mutane sun magantu a kansu
  • Ta nuno dan karamin akwati wanda a ciki ne ta biye kudaden na kasashe iri-iri, kuma yan Najeriya da dama sun ce ba za su iya aikata hakan ba
  • Daga cikin wadanda suka yi martani ga wallafarta akwai wadanda suka yi gode mata kan wannan abu da yi suma sun ce za su ajiye tsoffin kudin

Wata matashiya yar Najeriya mai suna @omowo a Twitter ta yada hotunan tsoffin kudi na N1000, N500 da N200 wadanda za ta ajiye saboda tarihi.

Ta kara da cewar za ta kara wadannan kudade a cikin jerin kudaden kasashen da ta taba ziyarta.

Matashiya da takardun kudi
Matashiya Ta Adana Takardun Tsoffin Kudi Saboda Tarihi, Hotunan Sun Haddasa Cece-Kuce Hoto: @omowo
Asali: Twitter

Matashiya ta adana tsoffin naira

Hotunan da ta wallafa a Twitter ya nuno wani hadadden akwati dauke da wasu kudaden kasashen waje da kwabo-kwabo a shirye a ciki.

Kara karanta wannan

Borno: ISWAP Sun Yi Rabon Tsofaffin Kudi ga Fasinjojin Motocin Haya Kyauta, Sun ce SU je Bankuna Su Canza su

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yan Najeriya da dama sun yi martani kan wannan yunkuri nata na boye tsoffin kudin. Yayin da wasu suka kalli abun a matsayin shawara mai kyau, wasu sun ce wannan ya yi yawa da za a ajiye na tarihi.

Kalli wallafar tata a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Winny_Cruz042 ta ce:

"Ta yaya zan ajiye har 1700 saboda tarihi? Kodayake wannan hoto naki zai zama nawa tarihin."

@IdleThumbz ya ce:

"Gaba daya wannan kudin ne zan ajiye a matsayin me ma kika kira shi? Tarihi wanda mutum zai iya nemansa a yanar gizo."

@Holarneyarn ta ce:

"Nima na yi wannan tunanin, amma talauci ya ce a'a."

@IfedayoOgunyemi ta ce:

"Mutumin da ke da kudi ne yake ajiye N1,700 dan sauransu a matsayin tarihi."

@monblaze ya ce:

"Na so yin haka amma bani da kudi da zan ajiye har N1700 a matsayin tarihi. Zan dauki hotunansu."

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Hankali Tashe Yana Nadamar Son Kudinsa, Yace Kwanaki Kadan Suka Rage ya Mutu

@_ayomid_ ta ce:

"Kada ki yarda ki rana shafin ki fa. Wannan ne nawa tarihin."

Bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin kudi, CBN

A wani labarin, gwamnan babban bankin Najeriya, Gowin Emefiele ya ce ko bayan cikar wa'adin daina amfani da tsoffin kudi, bankuna za su ci gaba da karbarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel