Canjin Kudi: Gwamnan CBN ya Isa Majalisa, Sun Shiga Ganawa

Canjin Kudi: Gwamnan CBN ya Isa Majalisa, Sun Shiga Ganawa

  • Bayan kwanaki da barazanar saka Sifeta janar ya kama Emefiele da kakakin majalisar dattawa yayi, Gwamnan CBN ya bayyana gaban majalisa
  • Daga zuwansa ya zauna gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar kan canjin kudi wadanda suka dinga nemansa ido rufe
  • Yayi bayanin cewa wadannan sabbin tsarikan an samar da su ne domin amfanin kasar nan balle a yayin da ake yakar rashin tsaro

FCT, Abuja - Gwamnan babban bankin Najerya, CBN, Godwin Emefiele, ya isa majalisar dattawan Najeriya, TVC News ta rahoto.

A halin yanzu sun shiga gawa da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da wasu manyan 'yan majalisar.

Godwin Emefiele
Canjin Kudi: Gwamnan CBN ya Isa Majalisa, Sun Shiga Ganawa. Hoto daga TVCnews
Asali: UGC

Emefiele yayin jawabi gaban kwamitin yayi bayanin cewa ba ya kasar ne shiyasa bai iya amsa gayyatarsu ba a baya.

A yayin jawabi kan sake fasalin wasu takardun Naira, yace abinda babban bankin tayi yayi daidai da tsarika mafi inganci kuma suna da damar juya kudin da ke yawo a gari, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu Gwamnati da Zata Iya Shawo kan Dukkan Kalubalen Najeriya ita Daya, Shugaba Buhari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Emefiele yace a 2015, N1.4 tiriliyan ce ke yawo a gari kuma a shekarar da ta gabata, lamarin yayi yawa inda N3.33 ke yawo a kasar nan.

Yayi bayanin cewa, dalilin da yasa suka kayyade kudin da za a fitar a rana shi ne a kayyade tare da kiyaye kudin da zasu shiga hannun jama'a.

Shugaban babban bankin ya koka kan sabon yayin da ya fito inda ake ganin sabbin kudin wurin shagalin bukukuwa kuma yace yana taruka da bankunan 'yan kasuwa don dakile hakan.

Dattijon mai shekaru 61 yace tsarikan tabbas za su batawa wasu mutane amma yayi ikirarin cewa hakan ne ya dace da kasar balle a yayin yaki da rashin tsaro.

Emefile ya gaza bayyana a gaban 'yan majalisar ne duk da gayyatarsa da suka dinga yi a wasku mabanbanta kan cewa yana Amurka don aiwatar da wani muhimmin aiki.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, har sai da ya kai matakin cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wurin umartar Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, da ya bada damar kama Emefiele don saka shi dole ya bayyana gaban majalisar.

A watan Nuwamba, babban bankin ya saka 31 matsayin wa'adin da kasar nan za ta daina amfani da tsofaffin takardun Naira.

Sai dai, karancin takardun Naira din ya tirsasa majalisar kafa kwamitin wucin-gadi domin shawo kan wannan matsalar tsakanin CBN da bankunan 'yan kasuwa duk da jajircewar Emefiele kan cewa bankuna ne ke boye sabbin kudin.

Mayakan ISWAP sun dinga raba tsofaffin kudi ga matafiya

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne a Borno sun tare babban titin Maiduguri inda suka dinga rabon kudi da matafiya.

Sun bukaci su je su canza su a bankuna sannan Allah kuma ya sanay musu albarka a cikin kudaden.

Asali: Legit.ng

Online view pixel