Hukumar Hisbah Ce Ta Daura Aurena Da Saurayin 'Diyata, Kuma Hakan Ba Haramun Bane: Khadija

Hukumar Hisbah Ce Ta Daura Aurena Da Saurayin 'Diyata, Kuma Hakan Ba Haramun Bane: Khadija

  • Kun ji labarin matar auren da ta kashe aurenta kuma ta auri tsohon saurayin diyarta a jihar Kano
  • Yan'uwanta sun kai kara wajen hukuma cewa a dawo musu da diyarsu saboda ba da izininsu tayi aure ba
  • Matar ta fadi ta bakinta kuma tace Malamai sun ba ta izini kuma hukumar Hisbah ta daura auren

Kano - Malama Khadija, matar da labarinta ya yadu ta rabu da mijinta don auren saurayin 'diyarta ta yi jawabi da labarinta dake yaduwa da kuma dalilin da yasa tayi hakan.

Wannan abu ya auku ne a karamar hukumar Rano ta jihar Kano.

‘Yanuwan matar a wani hira da suka yi a gidan rediyon Freedom sun bayyana cewa shugaban hukumar Hisbah ne ya daura auren ba tare da sa hannun waliyyanta ba

Kara karanta wannan

Hisbah ta kammala bincike kan labarin matar da ta auri saurayin diyarta a Kano, Ga sakamako

Jihar Kano
Hukumar Hisbah Ce Ta Daura Aurena Da Saurayin 'Diyata, Kuma Hakan Ba Haramun Bane: Khadija
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Malama Khadija

Bayan yaduwar labarin, Malama Khadija ta ce ita fa tana jin dadin aurenta da sabon miji kuma tana cikin koshin lafiya, riwayar Punch.

Ta ce dalilin da yasa ta aureshi shine ya hallata a addinin Musulunci kuma 'diyarta, Aisha, tace bata son shi, ita kuma tace gwanda ta aureshi kada dukkansu su rasa shi.

Tace:

"Ba da jahilci nayi ba. Na yiwa malamai fatawa kuma sun ce ba haramun bane a Musulunci. Sai na tuntubeshi (saurayin) kuma ya amince, amma iyayensa da yan'uwana suka ki daura mana aure."

"Shi yasa na yanke shawaran zuwa wajen Hisbah kuma munyi aure yanzu cikin farin ciki."

Jawabin 'yan'uwanta

Yayan Khadija, Abdullahi Rano, ya ce dalilin da yasa basu amince da auren ba shine da gayya ta kashe aurenta na farko don ta auri saurayin.

Kara karanta wannan

Soyayya Gamon Jini: Dirarriyar Matar Aure ta Bayyana Wadan Mijinta a Bidiyo, Tace Suna Cikin Farin Ciki

Yace:

"Sai da ta matsawa mijinta lamba ta sake ta don ta auri mutumin. Wannan abin kunya ne a danginmu kuma ba zamu amince da hakan ba a danginmu shiyasa muka ku yarda."
"Bamu ji dadin abinda Hisbah tayi ba kuma muna kira ga a dawo mana d adiyarmu."
Yayinda aka tuntubi kwamandan Hisbah na jihar, Sheikh Harun Ibn-Sina, ya ce zasu gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel