Ranar 4 Ga Watan Fabrairu Za a Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamnan PDP a Jihar Abia

Ranar 4 Ga Watan Fabrairu Za a Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamnan PDP a Jihar Abia

  • Jam’iyyar PDP a jihar Abia ta sanar da sake fara siyar da fom din takarar gwamna a jihar da ke Kudancin Najeriya
  • Allah ya yiwa dan takarar gwamnan PDP a jihar Abia, Farfesa Uche Ikonne bayan gajeriyar rashin lafiya
  • INEC ta ba da umarnin a gaggauta sake yin zaben fidda gwani don zabo wanda zai maye gurbin dan takarar na gwamna

Jihar Abia - Jam’iyyar PDP a jihar Abia ta sanya ranar 4 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar sake yin zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar, rahoton Punch.

Wannan na zuwa ne bayan da jigon jam’iyyar kuma mai rike da tutar takarar gwamna a jihar, Farfesa Uche Ikonne ya kwanta dama a cikin makon nan.

A cikin sanarwar da jam’iyyar ta PDP ta fitar a ranar Juma’a 27 ga watan Janairu, ta ce za ta sake zaben fidda gwanin gwamnan Abia ne a filin wasa na Umuahia.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamna Ya Tsallake Rijiya da Baya a Wata Jaha, An Bayyan Jam’iyyar Da Ta Farmake Shi

PDP za ta sake zaben fidda gwanin gwamna a Abia
Ranar 4 Ga Watan Fabrairu Za a Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamnan PDP a Jihar Abia | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A sanarwar da PDP ta fitar ta hannun mataimakin shugabanta, Abraham Amah, jam’iyyar ta bukaci dukkan masu sha’awar tsayawa takara su siya fom din takara kafin lokacin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An fara siyar da fom

A cewar sanarwar, duk mai bukatar tsayawa takara zai karbi fom a hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza a babban birnin tarayya Abuja, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar sanarwar:

“An fara siyar da fom a ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu kuma za a rufe a ranar Laraba 1 ga watan Fabrairun 2023.
“Za a yi taron tantance ‘yan takara a hedkwatar PDP ta kasa da ke Wadata Plaza a Abuja a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairun 2023 nda misalin karfe 11 na safe.
“Ana bukatar dukkan ‘yan talarar da su gana da kwamitin manyan ayyuka na PDP a jihar Abia a ranar Juma;a 3 ga watan Fabrairun 2023 a sakateriyar jiha da ke Titin Finbars a birnin Umuahia da misalin karfe 12:00 na rana.

Kara karanta wannan

Mafita: Dan gwamnan PDP ya rasu, INEC ta fadi yadda za a maye gurbinsa

“Duk sauran bayanai da ake bukata za a fade a sakateriyar jam’iyyar ta jiha da ke titin Finbars.”

INEC ta ce a sake zaben fidda gwani cikin kwanaki 14

A tun farko kunji cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta ba da umarnin a sake yin zaben fidda gwanin PDP a Abia.

Za a yi hakan ne saboda Allah ya yiwa dan takarar gwamnan jihar rasuwa bayan gajeriyar rashin lafiya.

Jama’a a kasar nan sun bayyana bukatar sanin halin da ake ciki bayan mutuwar wannan dan takara na gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel