Rudani a Kebbi Yayin da Wasu Manyan Jami’ai da Mataimakin Kakakin Majalisa Suka Yi Murabus

Rudani a Kebbi Yayin da Wasu Manyan Jami’ai da Mataimakin Kakakin Majalisa Suka Yi Murabus

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an samu tsaiko yayin da wasu jiga-jigan majalisa suka ajiye mukamansu nan take
  • Mataimakin kakakin majalisa na daya daga cikin wadanda suka bayyana barin mukamansu saboda wasu dalilai
  • Majalisar dokokin jihar Kebbi ta gayyaci gwamna don ba da bahasi game da kashe wasu manyan kudade a jihar

Jihar Kebbi - Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu jiga-jigan majalisar dokokin jihar Kebbi shida, ciki har da mataimakin kakaki Muhammad Usman sun yi murabus daga kujerunsu a ranar Alhamis 26 ga watan Janairun 2023.

An bayyana batun murabus din jigon majalisar ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Shehu Muhammad Yauri ya shaidawa manema labarai a Birnin Kebbi, Daily Nigerian ta ruwaito.

A bangare guda, majalisar jihar ta kuma nemi ganin gwamnan jihar domin ba da bahasi kan wasu kudaden da majalisar ta amince a ci bashi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Saura kiris zabe, dan takarar gwamnan PDP a wata jiha ya kwanta dana

Manyan jiga-jigan majalisa sun yi murabus
Rudani a Kebbi Yayin da Wasu Manyan Jami’ai da Mataimakin Kakakin Majalisa Suka Yi Murabus | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar wasikar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Manyan jiga-jigan majalisar dokokin jihar Kebbi, daga mataimakin kakaki, sun ajiye mukamansu.”

Mambobi 20 sun sanya hannu kan wasikar yin murabus

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, mambobi 20 cikin 24 na majalisar sun sanya hannu kan wasikar ajiye aikin wadannan manyan jami’ai.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya ce ya zuwa yanzu dai ba a bayyana dalilin ajiye mukaman na jami’an majalisar ba, rahoton PM News.

Hakazalika, ba a yada wata jita-jita da ke nuna ainihin dalilin da yasa manyan jami'an suka ajiye mukamansu ba.

Ana son ganin Atiku Bagudu ranar Juma’a

Wani rahoton NAN ya ce, an karanto wata wasika mai kwanan watan 26 ga watan Janairun 2023, magatakardan majalisar, Suleman Shamaki ya gayyaci gwamna Atiku Bakudu domin bayyana a gaban majalisar.

An ce ana son ganin gwamnan ne a yau Juma’a 27 ga watan Janairu domin ba da bahasi kan kudi N18.7bn na rance da majalisar ta amunce a ci a ranar 18 ga wtaan Oktoban 2021.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana tsadar abinci, dakin ajiyan kamfanin abinci ya kone kurmus

Bayan tsige mahaifinta a saraunta, kwamishiniyar Bauchi ta ajiye aiki

A wani labarin kuma, Hajiya Sa'adatu Bello Kirfi, kwamishiniya a jihar Bauchi ta bayyana ajiye mukaminta saboda wasu dalilai.

Ana kyautata zaton wannan yunkuri na Sa’adatu na da alaka da yadda gwamnan jihar ya tsige mahaifinta a matsayin Wazirin Bauchi.

Wata majiya ta shaidawa wakilin Legit.ng, al'ummar jihar bauchi ba sa tare da gwamnan wajen dakatar da mahaifin kwamishiniyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel