Yan Majalissar Wakilai Sun Bukaci Da A Dakatar Da Aiyiukan Jami'oi Lokacin Zabe

Yan Majalissar Wakilai Sun Bukaci Da A Dakatar Da Aiyiukan Jami'oi Lokacin Zabe

  • Majalissar wakilai ta bukaci da bawa dalibai hutu lokacin zabe dan su sami damar zuwa kada kuri'a
  • Dalibai dai kan iya bada ruwa a wannan zaben, domin akwai kiddidiga mai yawa kan sun fi kowa yawan katin zabe
  • Da yawan daliban manyan makarantun sakandire da na jami'oi hadi dana kwalejin ilimi ba a garuruwansu suke ba

Abuja - Yan majalissar dokokin tarayyar Nigeria sun bukaci da hukumar da ke kula da jami'o'in Nigeria NUC, da hukumar da ke kula da manyan makarantun gaba da sikandire NBTE, da kuma ma'aikatar ilimin tarayya da su dakatar da aiyukan karatu lokacin zabe.

Majalissar tace hakan zai bawa dalibai damar komawa garuruwansu dan gudanar da aiyukan zabe.

Majalissar ta kuma roki hukumar zabe kan ta tsara yadda daliban zasu karbi katinsu ba tare da matsala ba. Rahoton The Cable

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Tinubu Ya Daukarwa Iyaye Gagarumin Alkawari Da Zai Cika Masu a Kan 'Ya'yansu

Wannan dai na cikin kudirin da dan majalissa Kabir Ibrahim mai wakiltar mazabar Zuru/Fakai/Danko-Wasagu da Sakaba na jihar Kebbi ya kai gaban majalissar kamar yadda jaridar Tribune ta rawaito.

Danmajalissa
Yan Majalissar Wakilai Sun Bukaci Da A Dakatar Da Aiyiukan Jami'oi Lokacin Zabe Hoto: NASS
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan majalissar yace akwai kimanin dalibai kusan miliyan 2.1 da suke karatu yanzu haka a jami'oi da manyan makarantun gaba da sikandire hadi da manyan makarantun ilimi na tarayya da na jihohi.

Yace

"Akwai tsarin gudanarwar makarantun da ya ci karo da lokutan zabe ko kuma lokutan karbar katin zabe, dan haka muke rokon majalissa tai duba dan samar musu da hanyar da zasu karba kuma su jefa kuri'a"

Dalibai Miliyan 3.8 Suke Da Kuri'a

Dan majalissar yace bisa ga kiddigar bayanan da suke cikin kundin hukumar zabe na wanda sukai rijistar katin zaben, akwai kimanin dalibai miliyan 3.8 da sukai rijista katin zabe wanda kuma adadin nasu ya kai kaso 40 cikin dari na wanda sukai rijistar

Kara karanta wannan

Tinubu bai zagi Buhari ba, PDP da wasu yan jarida ke kokarin hada su rigima: Inji APC

Daliban nan da suke da kaso 40 cikin dari na masu kada kuri'a, basa kusa da akwatunansu da kuma mazabunsu, wasu kuma ma ba a jihar su suke ba, dan haka dole a bada hutun dan su samu damar zuwa guraben a zasu kada kuri'arsu"

Dan majalissar yace akwai kuma bukatar manyan makarantun gaba da sikandire da su samar da wani hutu a jaddawalin karatunsu dan bawa daliban damar zuwa inda zasu kada kuri'a

Asali: Legit.ng

Online view pixel