An Kama Wani Mutum Yana Kokarin Sace Janaretan Kotu a Jihar Ogun

An Kama Wani Mutum Yana Kokarin Sace Janaretan Kotu a Jihar Ogun

  • An kama wani matashi a jihar Ogun da ke shirin sace janaretan kotun jihar, ya amsa laifinsa yayin da aka kama shi
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai an mika matashin ga rundunar ‘yan sandan jihar
  • Ba wannan ne karon farko da ake kama matasa da sata ba, CCTV ta taba kama wani yana kokarin sace agogon masallaci

Jihar Ogun - An kama wani matashi mai shekaru 28, Folarunsho Olaniyan yayin da yake shirin sace janaretan kotun Kwastamare a Ado-Odo a karamar hukumar Ota ta jihar Ogun.

Jaridar Punch ta tattaro cewa, Olaniyan dan asalin yankin Ota ne, kuma magatakardan kotu, Kareem Tolulop ne ya kama shi dumu-dumu.

Majiya ta shaida cewa, wanda aka kaman an ce ya fasa ofishin kotun, inda aka adana janaretan a ranar 24 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

An kama matashi yana shirin sace janaretan kotu
An Kama Wani Mutum Yana Kokarin Sace Janaretan Kotu a Jihar Ogun | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An ce matashin ya yi saraf don yin satan ne saboda a ranar ana hutun aikidon ba kowa damar karbar katin zabe a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da kansa ya amsa laifin da ya aikata

Jami’a a ma’aikatar karamar hukumar, Mercy Ajewole ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an kama matashin nan take.

A cewarta, Olaniyan ya amsa laifin kutsawa cikin sakateriyar ta hanyar haura katanga, inda tace an mika shi ga ‘yan sanda, kafar labarai ta Reuben Abati ta ruwaito.

Ta kuma bayyana cewa, an gano kayayyakin kunce kusa da jaka a tare dashi., wanda ake zargin da su yayin amfani don fasa makudin kotun.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ba, SP Abimbola Oyeyemi.

Akan samu lokutan da matasa bata-gari ke aikata laifuka irin wadannan a yankuna daban-daban na Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana tsadar abinci, dakin ajiyan kamfanin abinci ya kone kurmus

CCTV ta kama wani yana kokarin sace agogon masallaci

A wani labarin kuma, an ga wani mutum a wani bidiyo lokacin da yake shirin sace agogon masallacin da ba a bayyana a ina ne ba.

Rahoton da muka samo ya ce, alamu sun nuna mutumin bai san da akwai kamera a cikin masallacin da ya yi satar ba.

Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi martani, sun bayyana abin da suka ji da ganin wannan mutumin da ke shirin barna a dakin ibada kuma na Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.