Na'urar CCTV ta nadi mutumi yana satar fitila a Masallaci

Na'urar CCTV ta nadi mutumi yana satar fitila a Masallaci

  • Faifan bidiyo ya nuna wani mutumi yana satar fitila a Masallaci
  • Na'urar CCTV ta nadi mutumin yayinda ya cire fitilar har ya gudu
  • Mutane sun yi mamakin ta wani dalili mutum zai saci fitilar Masallaci

Wani bidiyo daya yadu a kafafen sada zumunta an hangi wani mutumi yana sata a masallaci a yayin da yaje Sallah.

Mutumin yayi kamar zai tsugunna yayi ruku'u amma yayin da yaga ba wanda yake kallonsa kawai sai ya saci fitila.

Sai da ya hau chan sama kafin ya iya dauko fitilar saboda an rataya tane a chan saman bango daga nan ya tura ta cikin jakarshi.

Sannan yayi maza ya fice daga cikin masallacin.

Na'urar CCTV ta nadi mutumi yana satar fitila a Masallaci
Na'urar CCTV ta nadi mutumi yana satar fitila a Masallaci Hoto: Correctng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Takarar mataimakin shugaban kasa ko sanata: Makomar Ganduje bayan sauka a kujerar gwamna

Mutane sun kadu da ganin yadda mutumin ya rasa inda zaiyi sata sai wurin bauta.

Ga wasu daga cikin abinda mutane suka ce

tools.crispy yace; kai wannan ba fitila bace.

kosi_levi yace; Fitila ka sace a wurin bauta, kaii Abin bazai ma kyau ba

snowkween9 yace; A jininshi yake.

mc_nomicable yace; Fitila kuma, Haka abubuwa suka yi tsanani a kasar nan kenan.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel