Peter Obi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Da Man Fetur Din Da Aka Gano A Bauchi Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Peter Obi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Da Man Fetur Din Da Aka Gano A Bauchi Idan Ya Zama Shugaban Kasa

  • Peter Obi ya dauki alkawarin yin aiki da kudin danyen man da aka hako a Bauchi don ciyar da Bauchi da Arewa gaba
  • Dan takarar na LP, ya bayyana haka a taron gangamin yakin neman zaben da ya gudanar a Bauchi ranar Alhamis
  • Mr Obi ya kuma bukaci shugabannin kasar nan da su yi koyi da Tafawa Balewa wajen gudanar da mulkinsu don bunkasa Najeriya

Bauchi - Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar LP, Mr. Peter Obi, ranar Alhamis, ya tabbatarwa da alummar Jihar Bauchi cewa za ayi amfani da danyen man fetur din aka samu a jihar don ciyar da jihar da kuma yankin Arewa gaba.

Ya yi alkawarin ne a yakin neman zaben zaben jam'iyyar da ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa a Bauchi, babban birni Jihar Bauchi, a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

Peter Obi
Peter Obi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Da Man Fetur Din Arewa Da Aka Gano A Bauchi. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Za mu tabbatar an yi amfani da man don cigaban Bauchi, Peter Obi

Obi ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

''Mun san abin da yake faruwa a Bauchi a halin yanzu. Muna son yin amfani da danyen man da aka hako don cigaban Bauchi, da kuma baku ayyukan yi. Zamu tabbatar anyi amfani dashi don cigaban Bauchi, da cigaban Arewa, don tabbatar da komai yana aiki bawai mutum daya ya sace kudin yabar kowa a cikin yunwa ba.
''Ku fita ranar 25 (Fabrairu), ku zabi jam'iyyar Labour, ku nemi LP ku kuma zabi LP, anan za ku ga sabuwar Najeriya."

Ya bayyana cewa a duk lokacin da yake Bauchi, yana tuna masa lokacin da Najeriya take a matsayin kasa daya mai cike da zaman lafiya jihar ta fitar da daya daga cikin shugabannin da suka sanya kasar alfahari.

Kara karanta wannan

Ban Ba Yan Najeriya Kunya Ba, Inji Buhari Yayin da Yake Yi Wa Tinubu Kamfen

Tafawa Balewa ya yi imani da kasa daya, al'umma daya - Obi

Lokacin da yake bayyana Tafawa Balewa a matsayin shugaban da ya yarda da kasa daya al'umma daya, Obi ya yi takaicin cewa shugabannin kasar na yanzu sun mayar da kasar cibiyar yada talauci.

Da shugabani a yanzu zasu yi amfani da bashin da suke ciyowa kamar yadda Tafawa Balewa ya yi amfani da kudin da ya aro wajen gina Dam din Kainji, da Najeriya ta bunkasa, a cewar Obi.

Daga cikin tawagar dan takarar, akwai manyan shugabannin jam'iyyar ciki har da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Yusuf Datti Baba-Ahmed; shugaban jam'iyya na kasa, Julius Abure da kuma Pat Utomi, sun halarci taron

Asali: Legit.ng

Online view pixel