Uwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Bude Jakunkunan Makarantar Yaranta

Uwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Bude Jakunkunan Makarantar Yaranta

  • Wata mata yar Najeriya ta saki bidiyon kudaden sata da kayan wasan da ta gani a cikin jakunkunan yaranta
  • A wani bidiyo da ya yadu, ta nuna kudade yan N1000 da N500 jibge a daki da kuma cikin jakunkunansu
  • Yayin da take wallafa bidiyon, ta yi gargadin cewa ya kamata iyaye su zamo masu lura da tabbatar da bincikar yaransu

Wata uwa mai suna Keffe Arinola, ta saki wani bidiyo na kayayyakin da ta gano a cikin jakunkunan yaranta na makaranta.

A cikin bidiyon da aka daura a bidiyo, an gano kudade yan N1000 da N500 a cikin jakunkunan.

Mace da kayan wasan yara
Uwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Bude Jakunkunan Makarantar Yaranta Hoto: @keffearinola/TikTok
Asali: UGC

Uwar wacce ta cika da mamaki ta wallafa bidiyon kayan wasa da ke jibge a dakin yaran nata. A cewarta, suna ta sace mata kudade sannan suna amfani da shi wajen siyan kayan wasa iri-iri.

Kara karanta wannan

Bidiyon Baturiya Tana Yawo a Hargitse Babu Takalmi a Lagas Ya Girgiza Intanet, Bidiyon Ya Yadu

Ta yi gargadin cewa ya kamata iyaye su dunga sanya idanu sosai a kan yaransu sannan su dunga duba dakuna da jakunkunansu lokaci zuwa lokaci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta bayyana cewa babu 'kananan yara' a zamanin nan kuma kada a yarda da kowa.

Kalamanta:

"Ya kamata iyaye su dunga sanya idanu sosai a kan yaransu. Ku duba dakunansu cikin bazata, kada a yarda da kowa. Babu kananan yara a zamanin nan kuma, wannan ya sace mun gwiwa. Suna ta sace mani kudi sannan suna siyan abubuwa iri-iri."

Jama'a sun yi martani

@Princeyuan88 ya yi martani:

"Wannan abun ban dariya ne a wajena na rantse. Baaba abun da ya rage shine mutum ya shiga makaranta ka sanya bindiga a kansu sannan karbi kudi."

@Empress Becca ta ce:

"Allah ya kyauta."

@Alan chesterfield ta yi martani:

"Ban gane ba."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Uwa Ta Goya Yara 2 a Lokaci Guda Ya Dauka Hankali, Mutane Sun Jinjina Mata

@engrjayboi ya ce:

"Idan ya zamana mutane ke basu kyaututtukan kudin nan amma suka boye suka ki fada maki sannan suke siyan wadannan kayayyakin da su fa? Kiransu barayi da kika yi kadai ya tabbatar da cewar kina addabarsu sosai."

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, wani jami'in dan sanda ya sha jinjina a soshiyal midiya bayan ya tallafawa wani yaro mai lalurar tabin hankali.

Dan sandan ya dauki yaron ya wanke shi tsaf bayan ya yi masa askin gashin da ya taru a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel