Bayan Mutuwar Dan Takarar Gwamna, Waye Zai Maye Gurbinsa? Ga Abin da Doka Tace
- ‘Yan Najeriya sun shiga mamaki tare da jimamin rasuwar daya daga cikin ‘yan takarar gwamnan PDP
- Uche-Ikonne ya rasu ne kwanaki kadan gabanin zaben gwamnan da za a yi a Najeriya a watan Maris
- Dokar Najeriya ta tanadi wasu bangarori da ke nuna yadda za a sake gudanar da zaben fidda gwani don maye gurbinsa
Najeriya - Rasuwar Uche Ikonne, dan takarar gwamnan PDP a jihar Abia ka iya jawowa jam’iyyar tsaiko yayin da ake fuskantar zaben 11 ga watan Maris.
Ikonne ya mutu ne kusan wata guda kenan kafin zaben gwamna na shekarar 2023 da ake ciki.
Dansa, Dr Chikezie Uche-Ikonne ne ya tabbatar da mutuwarsa a yau Laraba 25 ga watan Janairun 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Wannan ba sabon abu bane ace dan takara ko kuma gwamna ya mutu a Najeriya, to amma ya batun maye gurbinsa zai kasance?
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abin da doka ta tanada
Watakila tanadin doka mai iya daukar lamari irin wannan shine sashe na 33 na kundin zabe.
Dokar ta ce, an haramtawa jam’iyyun siyasa sauya sunan dan takarar da tuni aka mika sunansa daidai da tanadin sashe na 29 na dokar zabe.
Sai dai, a lamarin da ke da alaka da janyewar dan takarar ko mutuwarsa, an ba jam’iyyar siyasa dama cikin kwanaki 14 ta sake yin sabon zaben fidda gwani tare da sake mika sunan dan takararta ga INEC.
Sashe na 34 (1) ya ce, idan aka samu mutuwar dan takara gabanin zabe ko bayan mika fom din takara, to kwashinan zabe na kasa zai duba tare da dage zaben, daga baya za ba da wani lokaci don sake yin zaben cikin kwanaki 14, rahoton Republic.
Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar PDP bata yi wani martani game da rasuwar wannan dan takara nata na gwamna ba.
Innalillahi: An yi babban rashi, 'yan bindiga sun kashe na hannun daman wani jigon APC
A wani labarin kuma, kunji yadda wasu 'yan bindiga suka kutsa har cikin gida suka hallaka wani jigon APC.
Wannan lamari ya haifar hargitsi, wani mutum a unguwar ya yanki jiki ya fadi bayan jin abin da ya faru.
Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba dabincike don gano wadanda suka yi kisan da kuma hukuntasu.
Asali: Legit.ng