'Yan Bindiga Sun Sheke Na Hannun Daman Tsohon Sakataren APC a Jihar Imo

'Yan Bindiga Sun Sheke Na Hannun Daman Tsohon Sakataren APC a Jihar Imo

  • Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun aikata mummunan aikin ta’addanci, sun sheke na kusa da shugaba a jam’iyyar APC
  • An hallaka mutumin ne a ranar Talata 24 ga watan Janairu, amma an bar matarsa da ‘ya’yansa a lokacin
  • Rahoto ya bayyana lamarin ya faru da kuma yadda wani daban ya tsorata ya fadi ya mutu a yankin da lamarin ya faru

Jihar Imo - Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun hallaka Christian Ihim, wani hadimin Emma Ibediro, tsohon sakataren shirye-shirye na jam’iyyar APC.

‘Yan bindihan sun kashe Ihim ne a gidansa da ke Umochoke Okwe a karamar hukumar Onuimo da sanyin safiyar ranar Talata 24 ga watan Janairu.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa TheCable cewa, matarsa da ‘ya’yansa dai sun tsira a wannan harin.

An hallaka jigon APC a Imo
'Yan bindiga sun sheke na hannun daman tsohon sakataren APC a jihar Imo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci Ya Ba Gwamnan CBN Mafita Kan Wa’adin Karbar Tsofaffin Nairori

A cewar majiya:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hadimi ne ga tsohon sakataren tsare-tsare na APC, Hon. Barr. Emma Ibediro daga Okwe. Yana kwance tare da iyalansa a cikin gida amma suka harbe shi ya mutu amma sun bar matarsa da ‘ya’yansa.
“Ni mutumin Okwe ne kuma na kwana a kauyen a wannan daren. Mun fito da safe suka ji wai wani mutum ya fadi tayel bayan jin harbin bindiga, ya fasa kansa.”

Shima mutumin ya mutu a asibiti da safe.

Ya kara da cewa:

“Akwai matsala a wannan kasar. Kullum kashe mutane ake kamar kaji. Yankin Onuimo ya daidaice saboda tsoro. Ya kamata gwamnati ta yi wani abu cikin gaggawa game da lamarin.”

A ranar Litinin, ‘yan bindiga sun kashe Chris Ohizu, shugaban karamar hukumar Ideato ta Arewa bayan karbar kudin fansa N6m daga iyalansa, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

‘Yan sanda a jihar Imo dai ya zuwa yanzu basu ce komai ba game da halin da ake ciki.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 Tare da Ceto Mutane 16 da Suka Yi Garkuwa da Su a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji yadda wasu 'yan bindiga suka gamu da tsaiko yayin da suka gamu da fushin sojojin Najeriya.

Rahoton da muke samu daga jihar Kaduna ya bayyana cewa, an hallaka 'yan bindiga uku tare da ceto wasu mutane 16 da aka sace.

Ana yawan hare-haren 'yan bindiga a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya cikin shekarun nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel