Ba Na Goge Hakorana: Kyakkyawar Baturiya Ta Magantu a Bidiyo Da Ya Yadu

Ba Na Goge Hakorana: Kyakkyawar Baturiya Ta Magantu a Bidiyo Da Ya Yadu

  • Wata matashiyar baturiya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta magantu a kan barin gidanta ba tare da ta goge hakoranta ba
  • A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano baturiyar tana tafiya cikin shiga ta sanyi a wata safiya
  • Wata budurwa ta tambaye ta ko ta goge horanta, sannan da take ba da amsa, ta bayyana cewa bata goge ba saboda ranar Lahadi ne

Wani bidiyon ban dariya na wata baturiya da ta yarda cewa bata goge hakoranta ba da safe bayan tashi daga bacci ya yadu a soshiyal midiya.

Baturiyar ta bayyana cewa koda dai ta ji kunyar bayyana cewa bata wanke bakinta ba a wannan safiyar, ta yanke shawarar fadin gaskiya duk dacinta.

Baturiya
Ba Na Goge Hakorana: Kyakkyawar Baturiya Ta Magantu a Bidiyo Da Ya Yadu Hoto: @orabrush/TikTok
Asali: UGC

A cikin bidiyon, an gano ta sanye da kayan sanyi lokacin da wata ta tsayar da ita sannan ta yi mata tambayoyi da ya shafi rayuwarta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Baturiya Tana Yawo a Hargitse Babu Takalmi a Lagas Ya Girgiza Intanet, Bidiyon Ya Yadu

An tambayeta ko ta wanke bakinta a wannan safiyar kuma matashiyar ta fadi gaskiya cewa bata wanke ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take kare kanta, ta bayyana cewa bata goge hakoranta bane saboda safiyar ranar Lahadi ne.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Alanna O’Grady ta yi martani:

"Tana da matukar kyau kuma na so yadda ta fadi iya gaskiyarta."

@selfobsessedscorpi0 ta rubuta:

"Wannan ne dalilin da yasa bana magana da mutanen da ban sani ba."

@higgside ta ce:

"Haka kuma bata yi wanka ba saboda ranar Lahadi ne."

@court ta yi martani:

"Ba na iya yin minti 5 da tsamin bakin nan na safiya."

@LydiaCallsen ta ce:

"Na so gaskiyarta."

@kokoshell ta rubuta:

"Ta yaya? Kamar ta yaya ba zan iya rayuwa da kaina ba ba tare da na goge baki da safe ba."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Uwa Ta Goya Yara 2 a Lokaci Guda Ya Dauka Hankali, Mutane Sun Jinjina Mata

@Sally Lynn ta ce:

"Akalla dai ta fadi gaskiya game da lamarin."

@Eri ta ce:

"Ban ga komai ba face koriyar iska."

@Georgia ta yi martani:

"Menene alakar Lahadi da kin goge hakora."

@skaiste virpalaite ya ce:

"Na kan goge bakine kawai kafin na kwanta bacci, sau daya a rana."

A wani labari na daban, jama'a sun yi cece-kuce bayan ganin bidiyon wata baturiya da ke yawo babu takalma kuma a hargitse a jihar Lagas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel