Ya Kamata CBN Ya Kara Wa’adin Mayar da Tsoffin Kudi, Direbobi a Gombe Sun Yi Kira Ga CBN

Ya Kamata CBN Ya Kara Wa’adin Mayar da Tsoffin Kudi, Direbobi a Gombe Sun Yi Kira Ga CBN

  • Direbobi a jihar Gombe sun bayyana kokensu tare da yin kira ga CBN da ta kara wa’adin mayar da tsoffin Naira
  • Sun koka da cewa, har yanzu bankunan kasuwanci na ci gaba da ba da tsoffin kudade a injunan ATM sabanin umarnin CBN
  • A tun farko an yi sauyin kudi, mayar da tsoffi da samun sabbi a Najeriya na ci gaba da daukar hankali a sassan kasar

Jihar Gombe - ‘Yan kabu-kabu a jihar Gombe sun yi kira ga Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa’adin da ya diba na daina amfani da tsoffin kudade a kasar nan.

Sun ce hakan zai ba da damar samun wadatattun sabbin kudade su yi yawo a hannun jama’a don rage wahalar harkallar yau da kullum a cikin al’umma, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karancin sabbin Naira: Kowa zai sha wahala, 'yan kasuwa a wata jihar Arewa za su dauki mataki

Da yake jawabi yayin shirin wayar da kan jama’a da CBN ya shirya a tashar mota da ke kwaryar jihar, direbobin sun koka da cewa, tsoffin kudi sun fi sabbi yawa a hannun jama’a.

Yadda direbobi ke kuka game da karancin sabbin Naira a Gombe
Ya Kamata CBN Ya Kara Wa’adin Mayar da Tsoffin Kudi, Direbobi a Gombe Sun Yi Kira Ga CBN | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani direba, Muhammad Sani ya bayyana cewa, adadin masu hawa mota da tsoffin kudade sun yi yawan masu zuwa tsoffin kudade tashar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankuna sun boye sabbin Naira, inji wani direba

Wani direba kuma mai suna Malam Ahmed ya bayyana zargin cewa, bankuna ne ke boye kudaden saboda wasu dalilai boyayyu.

A cewarsa:

“Wasu daga cikinmu sun je ATM, amma tsoffin kudi ake bayarwa sabanin umarnin CBN. Idan ka mayar da tsoffin kudi a cikin banki, sai su ce ka je ATM ka cire, amma injunan tsoffin kudi suke bayarwa."

Da yake martani ga batun direbobin, kwanturolan CBN a jihar Gombe, Shehu Alhaji Goringo ya shaida cewa, akwai isassun sabbin kudade da CBN ya bayar don a ba ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da walakin: CBN ya yi sabon batu game da karancin sabbin Naira da aka buga kwanan nan

Hakazalika, ya yi karin haske da cewa, CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su daina loda tsoffin kudade a injunan ATM.

Mutanen kauye sun rasa ta yi, babu sabbin kudi, sun kawo kaya kasuwa

A ziyarar da wakilin Legit.ng Hausa ya kai Kasuwar Tare da ke hanyar Bye Pass a jihar Gombe, ya tattauna da wani dillalin hatsi da ya bayyana masa halin da mutanen kauye ke ciki.

Kasancewar jiya Talata ranar kasuwa ce, an tambaye shi ya ba da bahasin yadda kasuwa ta kaya.

A cewar Alhaji Hussaini:

"Idan za ka kwatanta yanayin kawo kaya daga kauyuka, direbobi sun ba mutanen kauye ciwon kai, sun ki karbar tsohon kudi.
"Eh, wasu sun kawo kaya, amma basu yi ciniki da yawa ba, domin idan ka basu tsohon kudi ba sa karba saboda su ma ba a karbi nasu a mota.
"Yanzu a shagona, ina da ajiyar buhun masara sun kai 20 na abokai na ne na kauye, za su jira zuwa kasuwar ranar Juma'a ko za a dace."

Kara karanta wannan

Uwa Ta Fasa Asusun Yaranta Bayan Shekaru 10, Ta Fitar Da Tsoffin Kudi a Bidiyo

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.