Dan Sanda Ya Dauki Yaro Mai Tabin Hankali, Ya Yi Masa Aski Tare Da Gyara Shi a Bidiyo

Dan Sanda Ya Dauki Yaro Mai Tabin Hankali, Ya Yi Masa Aski Tare Da Gyara Shi a Bidiyo

  • Wani jami'in dan sanda ya sha jinjina a soshiyal midiya kan nuna kauna da ya yi wa wani yaro mai lalurar tabin hankali a titi
  • Jami'in tsaron mai zuciyar alkhairi ya ja yaron kusa da shi, ya kai shi ya masa wanka sannan ya yi masa akin gashin da ya taru a kansa
  • Bidiyon sauyawar yaron da jami'in dan sanda ya haifar da daddadan kalamai daga al'umma yayin da mutane suka yi masa addu'a

Wani jami'in dan sanda ya tsuma zukatan mutane da dama bayan wani karamci da ya yi wa wani yaro mai lalurar tabin hankali.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano dan sandan zaune kusa da yaron dauke da farin ciki a fuskarsa.

Dan sanda da mai lalurar tabin hankali
Dan Sanda Ya Dauki Yaro Mai Tabin Hankali, Ya Yi Masa Aski Tare Da Gyara Shi a Bidiyo Hoto: TikTok/@renita885
Asali: UGC

A shafukan da suka biyo baya, jami'in dan sanda ya samo almakashi sannan ya aske gashin kan yaron wanda ya yi babu kyawun gani kafin ya kai shi wani waje ya masa wanka da kansa.

Kara karanta wannan

Bana Ayyukan Ashsha: Matashin da ya Gina Tamfatsetsen Gida ya Fadi Sirrin Nasararsa a Bidiyo.

Yaron ya sauya gaba daya bayan kyakkyawar kulawar da ya samu daga wajen dan sandan. An gano jami'in tsaron mai zuciyar kirki rungume da yaron.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

linmakafui ya ce:

"Allah ya yi albarka ya kara maka tsawon rai ofisa."

lovely Baby ya ce:

"Dan Allah akwai wanda zai iya samo mun lambar dan sandan ina so na tallafa masa."

gabrieloduro663 ya ce:'

"Abun da nake son zama kenan a nan gaba mai taimako daga Allah."

@Qhuarbinartuga ya ce:

"Allah ya ci gaba da kare ka daga idon makiya."

NhaaDromoMaris ya ce:

"A duk lokacin da na ga abu irin haka, sai na kara jin karfi a Zuciyata cewa har yanzu akwai mutanen kirki Allah ya albarkace ka maigida muna bukatar mutane irinka."

Suruki ya yi wa angon diyarsa kyautar mota

Kara karanta wannan

Haihuwa Mai Rana: Matashi Dan Najeriya Ya Dankarawa Iyayensa Gida a Kauye, Bidiyon Ya Yadu

A wani labari, wani suruki ya yi wa angon diyarsa babban kyauta na kece raini a ranar daurin aurensu domin nuna jin dadinsa a kan auren yarsa da ya yi.

Angon dai ya samu kyautar mota ne kirar Land Rover sabuwa gal a leda inda mutane suka taya shi farin ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel