Miloniya Ya Yi Wa Angon Diyarsa Kyautar Sabuwar Mota Land Rover a Ranar Aurensu

Miloniya Ya Yi Wa Angon Diyarsa Kyautar Sabuwar Mota Land Rover a Ranar Aurensu

  • Wani fitaccen dan kasuwa, James Ndambo, ya y wa surukinsa babban kyauta bayan ya auri diyarsa
  • Ndambo ya ba surukinsa Emmanuel Izukanji Sichembe da Charmaine Ndambo Sichembe kyautar dalleliyar mota sabuwa fil
  • Lamarin ya kayatar da mahalarta bikin inda suka dungi daukar hotuna da bidiyoyin hadaddiyar motar

Kamar yadda aka saba gani a da, idan aka zo maganar aure, yan uwan miji ne ke da alhakin yi wa yan uwan amarya kyaututtuka da sha tara ta arziki.

Uban amarya ya yi wa ango kyautar mota
Miloniya Ya Yi Wa Angon Diyarsa Kyautar Sabuwar Mota Land Rover a Ranar Aurensu Hoto: Emmanuel Mwamba.
Asali: UGC

Sai dai kuma, zamani ya zo da sauyi sosai musamman a yanzu da samun wanda ze auri mutum ya yi wahala sosai.

Bin hanyar da ta dace

Wani shahararren dan kasuwa wanda ke matukar farin ciki ya nuna godiya ga surukinsa wanda ya nuna halin kirki a wajen auren diyarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

ANgo ya Sanar da Mutuwar Amaryarsa Bayan Kwana 11 da Shan Shagalin Aurensu, Hotunan Bikinsu Sun Girgiza Zukatan Jama'a

Fitaccen dan kasuwar Zambiya, James Ndambo ya yi wa mijin diyarsa kyautar wata dalleliyar mota kirar Land Rover sabuwa dal a leda.

"Kyautar nuna godiya kan auren diyarsa da ya yi da kuma bin hanyoyin da ya dace," wani bangare na rubutun da ke jikin bidiyon.

Salihin ango ya budewa amaryarsa mota

An gabatar da kyautar ga sabbin ma'auratan Emmanuel Izukanji Sichembe da Charmaine Ndambo Sichembe a ranar aurensu.

Jakadan Zambiya Emmanuel Mwamba ya bayyana cewa taken da aka yi wa kyautar shine "bijimi" yayin da ya taya ma'auratan murna.

An gano ma’auratan suna daukar hotuna da bidiyoyin hadaddiyar motar da aka baiwa ma’auratan.

Angon ya budewa amaryarsa mota kafin ya bi bayan motar sannan ya shige mazaunin direba.

Jama'a sun yi martani

Penelope Perez Mwansa:

"Wow. Ndambo mutumin kirki ne. Surukin ya yi dace da ya auri yar wannan gida. Na taya su murna."

MC Chiti Stewarts:

Kara karanta wannan

Bana Ayyukan Ashsha: Matashin da ya Gina Tamfatsetsen Gida ya Fadi Sirrin Nasararsa a Bidiyo.

"Yara mata nawa Ndambo ke da shi? Ina tambaya ne a madadin mijina Pack Muchi."

Chomba Mulunga

"Ina ji a jikina wannan mijin zai zama mai gaskiya. Ina nufin dole ya zama haka idan ya san me ya fi masa."

Alkyabbar mata: Bidiyon wata kyakkyawar budurwa mai ji da tsawo ya dauki hankali

A wani labarin kuma, mun ji cewa mabiya manhajar TikTok sun cika da matukar mamaki bayan cin karo da bidiyon wata budurwa mai tsawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel