Santala Uwar Tsawo: Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Mai Ji Da Tsayi Ya Ba Da Mamaki

Santala Uwar Tsawo: Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Mai Ji Da Tsayi Ya Ba Da Mamaki

  • Wata budurwa mai tsawon inci 6.5 ta yadu a TikTok bayan ta wallafa wani bidiyon da ke nuna tsayinta
  • Budurwar da ke da matukar tsawo na ban mamaki tana ta kokarin tabbatarwa mabiyanta cewa da gaske haka Allah ya halicce ta
  • Masu amfani da TikTok da dama wadanda suka ga bidiyonta suna shakku kan cewa mutum ba zai iya kasance da tsawo haka ba

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wata kyakkyawar budurwa mai matukar tsawo da ya kai inci 6.5.

Masu amfani da TikTok wadanda suka ci karo da bidiyon matashiyar mai suna @uceey3 suna ta tambayarta ko da gaske haka take saboda tsayin hotonta.

Budurwa mai ji da tsawo
Santala Uwar Tsawo: Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Mai Ji Da Tsayi Ya Ba Da Mamaki Hoto: TikTok/@uceey3.
Asali: UGC

Tana ta nanatawa masu shakku a kan tsawonta cewa babu inda yake ba na gaskiya ba a jikinta. Wasu mabiyanta basu yarda ba sannan suka bukaci ta motsa jikinta su gani kuma ta aikata hakan.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wani Mai Sahgo da Mahaukaciya ya ba jama'a Mamaki, SUn Dinga Hira kamar Tsofaffin Masoya

Bidiyon doguwar mace mai tsawon inci 6.5 ya yadu

A daya daga cikin bidiyoyinta, an gano ta cikin hadadden shiga sannan ta tsaya dauke fa dogon hotonta, lamarin da ya ba mutane mamaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bayananta na TikTok, ta bayyana kanta a matsayin 'yarinya mai ji da tsawon nan'. Bayanin ya yi daidai da ita don kuwa Allah ya yi mata baiwar tsayi.

Har yanzu ba a san yawan shekarunta ba, amma dai yanayinta ya nuna ita din matashiya ce kuma tuni ta yi fice a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@precieblack84 ta ce:

"Har yanzu ban yarda tsawonki ya kai haka ba."

@Pretty-@ntidote ta yi martani:

"Da ace watan Janairu Mutum ne haka zai kasance."

@user6909050036844 ya ce:

"Hajiya ba tsawo ne dake ba doguwa ce ke lol wasa nake yi kawai."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Uwa Ta Goya Yara 2 a Lokaci Guda Ya Dauka Hankali, Mutane Sun Jinjina Mata

@unreal______huncho ta tambaya:

"Ki na da saurayi."

@succy ta tambaya:

"Tsawon ki ya kai haka."

@aninoaganbi:

"Ma shaa Allah. kina da tsawo yarinya. Dan Allah ara mun tsayi kadan."

Iyayen amarya sun ki karbar tsoffin kudi a matsayin sadakin diyarsu

A wani labari na daban, iyayen wata budurwa a jihar Neja sun ki karbar kudin sadakin aurenta da iyayen manemin aurenta suka kawo.

Dalilinsu na kin karbar kudin shine cewa tsoffin kudade ne kuma ba su shirya kashe su kafin 31 ga watan Janairu da bankin CBN ya bayar a gama da tsoffin kudi a kasar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel