Na Yi Muku Hidima Gwargwadon Iyawata, Shugaba Buhari Ga ’Yan Najeriya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da sako ga ‘yan Najeriya kafin ya sauka daga karagar mulki nan da kwanaki
- Buhari ya ce ya cika alkawuran da ya dauka, domin kuwa babu abin da ke nuna bai yi hakan ba ga ‘yan kasar a mulkinsa
- Ya kuma yabawa shugabannin gargajiya a kasar nan, ya ce sun yi kokarin wajen ba shi goyon baya a shekarun mulkinsa
Jihar Bauchi - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta shekaru takwas abin yabawa ne ga ‘yan Najeriya.
Ya bayyana cewa, ya yiwa 'yan Najeriya hidima daidai gwargwadon iyawarsa kamar yadda kudin tsarin mulkin kasa ya tanada.
Shugaban kasan ya ce, duba da yadda ake haba-haba dashi a wurare da yawa, hakan ya nuna ya cika dukkan alkawuran da ya daukarwa ‘yan kasar, TheCable ta ruwaito.
Da yake zantawa a ranar Litinin a taron gangamin APC a jihar Bauchi, Buhari ya godewa sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu bisa ba shi goyon baya a shekarun mulkinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Buhari:
“Haka siddan nakan kira sarakuna da masu sarauta, ko dai a tafiyar siyasa ko ta kashin kai a jihohi don nuna godiya ta.
“Ina son fadi cewa a tsakanin 2003 zuwa 2011, na ziyarci kananan hukumomin kasar gaba daya, kuma a 2019 lokacin da nake neman a sake zaba na, na ziyarci dukkan jihohin kasar nan kuma mutanen da suke taruwa sun fi karfin a tara su saboda kudi ko karfi.
“Kuma acan, na yi alkawarin da rantsuwar zan yiwa Najeriya ‘yan Najeriya aiki iyakar kokari na kuma zuwa yanzu, ban ba ‘yan kasar kunya ba.”
Martanin sarkin Bauchi
A nasa bangarenm Sakin Bauchi ya yabawa Buhari, ya kuma ce mulkinsa abin koyi ne ga duk wani mai tunani a kasar nan, Arise Tv ta tattaro.
Ya kuma yabawa Buhari bisa kafa tsarin zabe babu ha’inci balle murdiya, inda yace ya yaba da irin ayyukan da ya yi a jihohin kasar nan a shekaru takwas na mulkinsa.
A kalamansa:
“Ba za mu iya kwatanta godiyarmu gareka ba kuma muna bin sahun gwamnanmu wajen mika godiyarmu.”
Boko Haram sun kare a Najeriya, inji Buhari
Daya daga abin da ya damu 'yan Najeriya shine Boko Haram, kuma shugaban ya ce a yanzu kam hakan ya kare a kasar.
Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da aka bashi lambar yabo a kasar Mauritaniya yayin da ya kai wata ziyara.
Duk da haka, ana yawan samun hare-hare a kasar nan daga 'yan ta'addan Boko Haram, lamarin da ke dagula zaman lafiya.
Asali: Legit.ng