Ganduje Ya Biya Bashin Kudin Makarantan Dalibai N18bn Da Kwankwaso Yaci

Ganduje Ya Biya Bashin Kudin Makarantan Dalibai N18bn Da Kwankwaso Yaci

  • Ganduje ya biyan Naira bilyan 18 cikin bashin kudin makarantar daliban jihar masu karatu a kasar waje
  • Gwamnatin yace tace Kwankwaso ya danawa Ganduje tarko saboda tarin basussukan ya bar masa
  • Kwamishanan labaran jihar yace idan mataimakin gwamnan Kano ya zama gwamna zai gyara tsarin

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya biya bashin kudin makarantun daliban jihar da gwamnan maigidansa, Rabi'u Musa Kwankwaso ta tura kasashen waje.

Kwamishanan labaran jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana haka a jawabin da ya fitar jiya, rahoton TheNation.

Ya bayyana cewa kudin N18bn, bashi ne na kudin makarantan dalibai yan asalin jihar Kano da ke karatu a kasashen waje.

Ya ce mafi akasarin daliban na karatu ne a kasar Faransa, Cyprus, da Masar.

Ganduje
Ganduje Ya Biya Bashin Kudin Makarantan Dalibai N18bn Da Kwankwaso Yaci Hoto: Kano
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Garba ya ce gwamnatin Kwankwaso ce ta fara wannan tsari amma ta ki biyan dalibai kudin.

A cewarsa:

"Lokacin da muka hau mulki a 2015, mun samu dimbin bashin kudin daukar nauyin karatun dalibai da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta bari kuma wannan abu ya bamu matsala."
"Amma mun biya kimanin N18bn kawo yanzu."

Garba ya caccaki gwamnatin Kwankwaso bisa yadda ta tura dalibai kasashen waje karantar ilmin da akwai su a Najeriya kuma a farashi mai arha, riwayar Tribune.

Yace gwamnatin Ganduje bata ki a tura dalibai kasar waje karantar ilmin da babu a Najeriya ba, amma rashin tunani ne a tura dalibai karantar ilmin tarihi a kasar waje.

Yace gwamnatin Kwankwaso bata bi tsarin da ya kamata wajen tsara shirin ba kuma akwai cakwakiya ciki.

A cewarsa, idan Gawuna ya samu nasarar danewa mulki, zasu gyara wannan tsari.

Yace:

"Idan aka zabi Gawuna matsayin gwamnan Kano, ko shakka babu zai yi dubi cikin shirin kuma ya gyara. Daliban da zasu amfani karatukan da zasu amfani jihar kadai zasu yi."

Kara karanta wannan

Gwamna Masari Ya Fitar da N500m don tara jama'a su tarbi Shugaba Buhari Ranar Alhamis

Mun san arzikin Kwankwaso ya Shigo Gwamnati Da Kuma Lokacin ya bar gwamnati

A wani labarin kuwa, mai takarar kujerar gwamnan jihar kano a jam'iyyar Labour Party LP, Bashir Ishaq, ya yi bayani game da abubuwan da gwamnatocin Kano da suka shude suka yi.

Yace sun san yadda gwamnonin baya suka azurta kansu yayinda suka hau mulki ta yadda suka zama masu kudi lokacin da suka bar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel