Dan Takarar Gwamna A Jam'iyyar LP A Kano Yace Gwamnatin Shekarau Da Kwankwaso Sunyi Kuskure

Dan Takarar Gwamna A Jam'iyyar LP A Kano Yace Gwamnatin Shekarau Da Kwankwaso Sunyi Kuskure

  • Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar SDP ya zargi gwamnatocin baya da rashin ko kula da wasu fannin rayuwa
  • Yan takara dai na jefa tare da sukan junan su kan wasu kudiri da suke ganin kaman basu dace da su ringa aiwatar da su ba
  • Ana shirya muhawarar ne dan jin bahasi da kuma manufofin da yan takarar suke da shi ga al'ummominsu

Kano - Dan takarar gwamnan jihar kano a jam'iyyar LP, ya magantu kan abubuwan da gwamnatocin baya na jihar Kano suka aikata a gwamnatocin baya da suka shude.

Bashir Ishaq wanda yake wa jam'iyyar Labour Party takarar ya magantu ne a wajen muhawarar yan takarar gwamna da cibiyar nazari da buinkasa harkokin mulki ta mumbayya ta gabatara na tsawon kwana biyu a tsakanin yan takarar gwamnan jihar Kano a kano.

Kara karanta wannan

Makiyan Jihar Bauchi Ne Kadai Za Su Zabi Dan Takararmu, Inji jiga-Jigan APC Da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP

Muhawarar wanda yan takarar gwamna su 11 suka bayyanawa jama'a manufofinsu da abunda zasu yi idan aka zabe su.

An shirya muhawarar ne tsawon kwana biyu domin raba yan takarar sabida samun damar jin ta bakin kowanne a cikinsu.

Dan Takarar LP
Dan Takarar Gwamna A Jam'iyyar LP A Kano Yace Gwamnatin Shekarau Da Kwankwaso Sunyi Kuskure Hoto: Legit.ng Hausa
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar farko yan takarar guda uku ne daga cikin biyar suka halarci zaman ciki akwai dan takarar labour Party, Bashir Ishaq, da na jam'iyyar APM, Sani Ibrahim da kuma wakilcin dan takarar ZLP, wanda Sunusi Ahmed Ya wakilta.

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar NNPP bai samu halarta muhawarar ba sabida yawan kamfe da yace ya shirya zai je.

Bayanin dan takarar LP

Yace akwai masana'antu a jihar Kano wanda suke a rufe kusan 576 da suke a rufe basa aiki kokadan, sabida rashin wuta ko kuma makamashin da kamfanonin suke bukata.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Dama Yayin Da Ake Tsaka Da Yakin Neman Zabe

A dalilin haka yasa dan takarar yace yayi alkawarin samar da gidan wuta mai karfin watt 100, sannan yasha alwashin cewa zai inganta harkokin noma.

Bashir yace

"Akwai kuskure mai girma kan abubuwan da gwamnatocin da suka shude na Shekarau Da kwankwaso sukai, wajen gina makarantu ba tare da bun kasa wanda ake da su ba"

Bashir yace:

"Mun san yadda gwamnatocin da suka shude suka shigo gwamnati da kuma yadda suka bar gwamnatin"

Bashir ya ci gaba da batun tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Kwankwaso yace:

"Ina mutum yake da rumfa ko kuma wani shago a kasuwa, muna sane da yadda mutanen nan suka shigo gwamnati da kuma yadda suka barta"

Shima a nasa jawabin manufofin dan takarar gwamnan jihar na zam'iyyar APM, Sani Ibrahim yace

"Zansa dokar ta baci akan harkokin ilimi, lafiya, muhalli da kuma zamantakewa"

Asali: Legit.ng

Online view pixel