Dangin Amarya Sun Ki Karbar Tsohon Kudi a Matsayin Sadaki a Neja

Dangin Amarya Sun Ki Karbar Tsohon Kudi a Matsayin Sadaki a Neja

  • Yan uwan wata matashiyar budurwa a jihar Neja sun ki karbar sadakinta da aka gabatar masu saboda dangin ango sun kawo tsoffin kudi
  • Dangin yarinyar sun ce sai bayan wa'adin 31 ga watan Janairu da CBN ya bayar za su kashe kudin don haka ba za su iya karbar tsoffin kudi ba
  • Sun kuma ce su basu da asusun ajiyar kudi na banki da za su iya kai kudin saboda haka idan dangin angon sun samu sabbin kudin sai su sake dawowa

Niger - Dangin wata amarya a karamar hukumar Gbako ta jihar Neja sun bukaci dangin mai neman aurenta da su zo su karbi tsoffin kudi yan N1000 da 500 da suka bayar a matsayin sadaki.

An tattaro cewa dangin angon sun kai wa dangin amarya wasu kudade a matsayin sadaki da sauran kayan aure yayin da ake shirye-shiryen biki.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Mutane Za Su Koma Sayen Litar Fetur a Kan N800 Nan da Watanni 6

Sabbin naira
Dangin Amarya Sun Ki Karbar Tsohon Kudi a Matsayin Sadaki a Neja Hoto: @drpenking
Asali: UGC

Dalilinsu na kin karbar sadakin amaryar

Koda dai ba a daga daurin auren ba, iyayen yarinyar sun bayyana cewa basu shirya siyan wasu abubuwan bukata na bikin ba kuma ga shi bankin CBN ya ba da wa'adin 31 ga watan Janairu na daina karbar tsoffin kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma sun ce basu da asusun bankin da za su zuba kudin a ciki don haka suka bukaci lallai sai dai a kawo sabon kudi, rahoton Daily Trust.

Wani dangin ango ya yi bayanin cewa:

"Mun kai kudin ga dangin yarinyar da muke son aure. Sun kira ni a ranar Lahadi cewa na zo na karbi tsoffin kudin har zuwa lokacin da za mu samu sabbi.
"Sun ce basu da inda za su je su chanja tsoffin kudin. Don haka ina so na kai kudin banki har zuwa lokacin da za mu samu sabbi."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Ya ci gaba da bayyana cewa mutane da dama na tsoron karbar tsoffin kudin don gudun cewa ba za su iya kashe su ba kafin ranar 31 ga watan Janairu.

Wasu yan kasuwa sun daina karbar tsoffin kudi

Aminiya ta kuma rahotocewa yan kasuwa a yankunan kakkara sun fara kin karbar tsoffin kudi wasu ma sun fara rufe kasuwancinsu saboda bankuna na ci gaba da bayar da tsoffin kudi.

A garin Zungeru da ke karamar hukumar Wushishi ta jihar Neja, mazauna sun ce banki daya ne a yankin duk da yawan mutane da hada-hadan kasuwanci da ke gudana a garin, musamman ma a lokacin cin kasuwanni Lahadi da Laraba.

Yan kasuwa sun bayyana cewa manoma sun daina kawo albarkatun gonarsu kasuwar Zungeru a ranakun Laraba da Lahadi saboda tsoron cewa za a basu tsoffin kudi.

legit.ng ta zanta da wasu yan kasuwa a garin Minna da ke jihar Neja don jin yadda abun yake a bangarensu.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: CBN ya kawo mafita ga mutanen kauye, ya kawo wani sabon tsari mai kyau

Malam Umar Malami ya ce:

“Gaskiya muma mun fara tunanin zuwa dan gajeren hutu saboda gaba daya a jiya da na fito kasuwa mutanen da suka kawo mana sabbin kudade basu fi a kirga ba. Kowa tsoffin kudadden yake kawowa kan hujjar cewa shima abun da ya samu kenan daga POS ko banki.
“Da dai za a kara wa’adin da zai fi amma gaskiya muna tsoron karbar tsofaffin kudin a yanzu don gudun tafka asara.”

A nata bangaren, wata mata da ke siyar da kayan hatsi ta ce:

“Muma yanzu idan mun je siyan kaya a kauye basa son karbar tsoffin kudi saboda sun ce babu inda za su kai a chanja masu don banki sai a cikin gari. Tun safe mutane sai kudin da suke kawo mana, gwamnati ta duba mana wannan abu don ana so a ja mana bala’i ne.”

Ba na burushi a ranar Lahadi, Budurwa

A wani labari na daban, jama'a sun bayyana albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wata matashiya da ta ce bata goge hakoranta a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel