CBN Ya Kaddamar da Shirin Musayar Sabbin Kudi da Tsoffi a Fadin Kananan Hukumomin Najeriya

CBN Ya Kaddamar da Shirin Musayar Sabbin Kudi da Tsoffi a Fadin Kananan Hukumomin Najeriya

  • Babban Bankin Najeriya ya kaddamar da wani shirin da zai taimakawa mutanen kauye wajen musayar kudadensu cikin sauki
  • An ba wasu kamfanoni lasisi don yin hada-hada da sauya tsoffin kudi ga mazauna kananan hukumomin Najeriya
  • Wannan shiri zai taimakawa mazauna kauyuka don kaucewa asarar ci gaba da ajiye tsoffin kudin da za a daina karba nan da kwanaki takwas

Najeriya - A kokarin tabbatar da yaduwar sabbin Naira, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kaddamar da shirin musayar kudi a kananan hukumomin Najeriya.

CBN ya ce wannan shirin zai fara ne daga ranar Litinin 23 ga watan Janairun 2023, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa, za a yi musayar tsoffin N200, N500 da N1,000 da sabbin bugun da aka buga watan Disamban bara da kuma tsoffin kananan kudade da ake kashewa a kasar.

Kara karanta wannan

Assha: Ana batun sabbin Naira na kodewa, hotuna sun nuna rashin daidaito a bugun

Shirin CBN zai taimakawa mutanen kauye
CBN Ya Kaddamar da Shirin Musayar Sabbin Kudi da Tsoffi a Fadin Kananan Hukumomin Najeriya | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

CBN ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wata takardar umarni da ya aikewa dukkan DMBs da masu hada-hadar kudi da manyan wakilansa a fadin kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, wannan shirin musayar kudi dai hadin gwiwa ne tsakaninsa da wakilansa da masu ahda-hadar kudi a bangarori daban-daban na kasar.

An ba wasu lasisin karbar tsoffin kudi su ba da sabbi

Dama tun farko, CBN ya ba wasu kamfanoni lasisin karba da iya sarrafa kudade a madadinsa a fadin kasar nan, rahoton Daily Post.

A baya-bayan nan, babban bankin ya kaddamar da shirin wayar da kan jama’a a Najeriya don ilmantar dasu halin da ake ciki game da sabbi da tsoffin kudi.

A cikin makon da ya gabata, babban bankin ya sha alwashin ladabtar da bankunan kasuwanci da suka ki zuwa daukar sabbin kudaden da aka buga don rabawa kwastomominsu.

Kara karanta wannan

Daga karshe: CBN ya fadi kudaden da zai caji bankuna a kullum kan kin daukar sabbin Naira

Ku sani cewa, wa’adin da CBN ya bayar na daina amfani da tsoffin kudi zai kare ne daga ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki.

Yadda shirin musaya zai kasance

Babban bankin ya shaida cewa, masu musayar za su amince da yiwa mutane canji ne daga N10,000 ya yi kasa, idan kudi ya haura adadin, sai dai a zubawa mutum a asusun banki.

Hakazalika, an ce wakilan CBN da masu hada-hadar za su wayar da kan jama’a domin bude asusun banki, ko ‘wallet’ na ajiyan kudi yayin gudanar shirin musayar.

A bangare guda, bankin ya ce ba za a caji duk wanda ke son sauya tsoffin kudadensu zuwa sabbi ko zuba su a banki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel