An Bar Mutane Cikin Rudani Yayin da Gwamnati Ta Fadi Gaskiyar ‘Karin’ Kudin Fetur
- Karamin Ministan man fetur yace Shugaban kasa bai amince a kara ko sisi a kan farashin litar fetur ba
- A wani jawabi da ya fitar, Timipre Sylva ya ce Muhammadu Buhari ya yi alkawari farashi ba zai tashi ba
- Sylva ya nuna a yadda aka tunkari babban zabe, Gwamnati ba za ta karawa talakawa wahala ba
Abuja - Gwamnatin tarayya ta shaida cewa babu wani karin farashin man fetur da aka yi, hakan na zuwa ne a lokacin da ake fama da karancin mai.
Punch ta ce Karamin Ministan harkokin mai, Timipre Sylva ya fitar da jawabi na musamman a yammacin Juma’a, ya musanya batun yin karin kudi.
A jawabin da Cif Timipre Sylva ya fitar dazu a garin Abuja, ya tabbatar da Mai girma Muhammadu Buhari bai amince a kara kobo kan kudin litar mai ba.
Ministan ya bayyana wannan ta bakin Hadiminsa, Horatius Egua a ranar 20 ga Junairu 2023.
Jawabin Timipre Sylva a kan rade-radin
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai amince da karin kudin fetur ko wani mai ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babu dalilin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fasa cika alkawarin da ya yi na kin amincewa da wani karin man fetur a halin yanzu.
Mai girma Shugaban kasa yana damuwa da halin da talaka yake ciki, kuma ya maimaita sau daya cewa ya fahimci kalubalen talakan Najeriya.
Saboda haka ba za iyi wani abin da zai zama kara azaba a kan wadanda suke kada kuri’a ba."
- Timipre Sylva
Kafin ayi kari sai an zauna tukuna
Nairametrics ta ce Ministan ya kara da cewa a wannan yanayi, gwamnati ba za ta canza farashi a asirce ba tare da an zauna da masu ruwa da tsaki ba.
Sylva ya ce Muhammadu Buhari bai umarci NMDPRA ko wata hukuma ta fadawa ‘yan kasuwa su kara farashin abin da suke saida litar fetur a kasar ba.
Kamar yadda aka rahoto, Ministan yana zargin wasu miyagu ne suka kirkiro labarin saboda kurum a rusa nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a fannin.
N170 zuwa N185
A wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta aikawa ‘yan kasuwa, an umarce su da suka kara kudin mai. Wannan shi ne rahoton da muka fitar a baya.
Da labarin ya tabbata, a maimakon N170, za a rika bada sarin litar man fetur a tashoshi a kan N185, da hakan zai jawo farashin saida fetur ya karu.
Asali: Legit.ng