Hatsari Ya Ritsa Ya Tawagar Motoccin Shahararren Gwamnan Arewa A Hanyar Zuwa Kamfe, Yan Majalisa Sun Jikkata
- An yi hatsari a cikin ayarin motoccin gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom a ranar Juma'a 20 ga watan Janairu
- Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon kwacewa da mota ta yi daga hannun wani direba cikin tawagar gwamnan
- Wasu yan majalisar tarayya da ke cikin tawagar a hanyarsu na zuwa kamfe a garin Igumale sun jikkata
Jihar Benue - Tawagar motoccin Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ta yi hatsari da garin Utokon da ke karamar hukumar Ado na jihar a ranar Juma'a.
Ortom da tawagarsa na hanyarsu na zuwa kamfen din dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Igumale, hedkwatar Ado, ne a lokacin da abin bakin cikin ya faru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta rahoto cewa motar ta kubce wa direban motan da ke makil da magoya bayan PDP ya buga wa wata Jeep, wata motar jami'an tsaro da wata bas cikin tawagar gwamnan.
Yan majalisa da jiga-jigan PDP sun jikkata sakamakon hatsarin
Motoccin da ke cikin tawagar sun hada da na mataimakin gwamnan jihar, Injiya Benson Abounu, Sanata Abba Moro, Mambobin majalisar wakilai na tarayya da yan majalisar dokokin jihar Benue, da wasu manyan jami'an gwamnati da jam'iyyar PDP a jihar.
Amma, ba da dadewa ba motar asibiti na gwamnatin jihar ta isa wurin da abin ya faru ta kwashe wadanda abin ya shafa ta tafi da su asibiti don yi musu magani.
A watan Maris na 2020, yan bindiga sun kai wa tawagar Ortom hari a Tyu Mu kan hanyar Makurdi-Gboko yayin da ya tafi ziyartar gonarsa.
Harin da aka kai wa Ortom ya janyo maganganu sosai a kafafen watsa labarai.
Da ya ke bada labari a lokacin, Ortom ya ce yan bindigan kimanin su 15 sun rika bin tawagarsa a baya-baya har zuwa bakin rafi inda shi da tawagarsa suka sauka don duba gona, suka bude musu wuta.
Daga baya yan sanda sun kama mutum 10 da hannu a harin.
Ortom ya yi magana kan yarjejeniyar da aka ce G5 ta yi da Bola Tinubu na APC
A wani rahoton, Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya ce babu wata yarjejeniya da G5 ta cimma da Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC.
Rahotanni sun fito da ke nuna cewa gwamnonin na G5 sun yi yarjejeniya da Tinubu yayin da suka gana a Landan.
Asali: Legit.ng