Atiku, Tinubu, Obi: Sarkin Musulmi Ya Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Ke Goyon Baya? Gaskiya Ta Fito
- An karyata rahoton da ya fito na cewa Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, ya goyi bayan wani dan takarar shugaban kasa gabanin zabe
- Sanarwa da ta fito daga tawagar watsa labarai na Sultan din ta bayyana ikirarin a matsayin rashin sanin ya kamata da ba za ta iya fitowa daga sarkin ba
- Sultan din ya jadada cewa ba zai yarda a jefa shi cikin siyasa ba yayin da ya gargadi wadanda ke yada labaran karya game da shi
Sokoto - Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, Sarkin Musulmi, ya nesanta kansa da wani rahoto da aka ce wai ya goyi bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour bisa Bola Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP da sauran.
Sarkin na Musulmi ya ce ba zai yarda a jefa shi cikin siyasa ba yayin da ya gargadi masu yada labaran karya kan cewa ya goyi bayan wani dan takarar shugaban kasa su dena, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin Sarkin Musulmi ya goyi bayan Obi, Tinubu ko Atiku?
Bashir Adefaka, daga tawagar watsa labarai na Sultan din ya bayyana matsayar sarkin gargajiyar da musulunci a cikin sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba.
Adefaka ya ce sanarwar da ke yaduwa a dandalin sada zumunta mai taken, 'Da Duminsa: Sultan na Sokoto Ya Yi Rubutu', ba komai bane illa karya.
Sultan din ya tunatar da yan Najeriya cewa wannan ba shine karo na farko ba da ake fitar da irin wannan sanarwar don yan siyasa su yi amfani da karfin iko na shugabannin addini.
Abin da ke faruwa a baya-bayan nan dangane da Bola Tinubu, APC, Atiku Abubakar, PDP, Sarkin Musulmi, Zaben 2023, Peter Obi, Jam'iyyar Labour, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar
Wani sashi na sanarwar da tawagar watsa labaran ta fitar ya ce:
"Abin takaici ga yan siyasan nan abin tausayi, Sultan na Sokoto - zancen gaskiya - basaraken gargajiya ne kuma jagoran musulmi a kasar Afirka mafi yawan al'umma. Kuma, kasancewarsa Janar din soja mai ritaya, tarbiyarsa da jajircewa da biyayya ga Najeriya ba abin shakka bane."
Adefaka ya kara da cewa irin wannan rubutu na rashin tarbiyya ba zai iya fitowa daga Sultan din ba kuma yan Najeriya su yi watsi da shi.
Helen Boco Ta Fita Daga Jam'iyyar APC Ta Koma PDP
A gefe guda, tsohuwar yar takarar mataimakiyar gwamnan a zaben shekarar 2019 a jihar Cross Ribas a APC, Helen Boco ta koma jam'iyyar PDP.
Boco ta sauya shekar ne yayin da ya rage kwanaki 49 a yi babban zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023, rahoton Tribune.
Asali: Legit.ng