Jam'iyyar APC Ta Umurci Mambobinta Su Yi Azumin Kwana 7 Saboda Neman Nasara A Kotu

Jam'iyyar APC Ta Umurci Mambobinta Su Yi Azumin Kwana 7 Saboda Neman Nasara A Kotu

  • Jam'iyyar All Progress Congress, APC, reshen jihar Osun umurci mambobinta su fara azumi da addu'a na kwana 7
  • Tajudeen Lawal, mukadashin shugaban jam'iyyar APC na jihar Osun ne ya bada wannan sanarwar a ranar Juma'a
  • Lawal ya ce sun kammala duk abin da za su iya a kotun zabe na neman kwato nasarar Oyetola, babu abin da ya yi saura sai addu'a

Jihar Osun - Jam'iyyar APC ta jihar Osun ta bukaci mambobinta su fara azumin kwana bakwai da addu'o'i, daga ranar Juma'a don neman nasarar Allah a shari'ar da kotun sauraron karar zabe ke yi, rahoton The Punch.

Kotun karkashin Mai Shari'a Tetse Kume ta kammala zamanta kan karar da tsohon gwamna Adeboye Oyetola da APC suka shigar na kallubalantar nasarar Sanata Ademola Adeleke na PDP a zaben 16 ga watan Yulin 2022.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

Adeleke da Oyetola
Jam'iyyar APC Ta Umurci Mambobinta Su Fara Azumin Kwana 7 Saboda Neman Nasara A Kotu. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Mun gama abin da za mu iya a kotu, yanzu Allah muke roko ya bamu nasara, Lawal

Ana fatan kotun za ta yanke hukuncinta kafin karshen watan Janairun 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwa da mukadashin ciyaman din APC na jihar, Tajudeen Lawal, ya fitar a Osogbo a ranar Juma'a ta ce:

"Ya zama dole jam'iyyar ta koma ga Allah tunda ta kammala duk abin da za ta iya yi a karkashin doka a kotun zabe don kwato nasarar Gwamna Oyetola da aka sace a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Yulin 2022."

Shugaban APC din na Osun ya kuma jadada muhimmancin addu'a wurin samun nasara da kare kai daga masu sharri.

Da ya ke kira ga yan APC din kada su yi wasa da azumin da addu'a, Lawal ya ce yana da karfin gwiwa cewa Allah amsa addu'arsu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kashim Shettima Yana Ganawar Sirri Da Rochas Okorocha A Abuja

Ya kuma yi kira ga yan jam'iyyar na APC su cigaba da yi wa Oyetola da mataimakinsa, Bennedict Alabi, da sauran iyalansu addu'a yayin azumi da addu'o'in da ya bada shawara.

Ya kuma umurce su da yin addu'a don jihar ta dawo da martabarta cikin sauran jihohi a tarayyar Najeriya.

Kotu ta soke zaben cikin gida na gwamnan PDP a Zamfara

Kun ji cewa kotun daukaka kara a Sokoto ta yi fatali da karar da PDP ta shigar game da zaben fidda gwamna da aka yi a Zamfara.

Mai shari'a Muhammad Shuaibu, cikin hukuncinsa ya jadada soke Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna na PDP, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel