Zan Yi Murabus a Matsayin Shugaban Twitter da Zarar Na Samu ‘Ba Hamagen’ Magaji, in Ji Elon Musk

Zan Yi Murabus a Matsayin Shugaban Twitter da Zarar Na Samu ‘Ba Hamagen’ Magaji, in Ji Elon Musk

  • Mamallakin kamfanin Twitter, Elon Musk ya bayyana matsayarsa kan ajiye mukaminsa na shugaba
  • Elon Musk ya ce, yana neman wanda zai iya karbar kujerarsa domin ci gaba da shugabantar kamfanin
  • Jama’a sun yi martani, sun ce babu abin da yafi dacewa kamar Muk ya sauya daga shugabancin kamfanin

Elon Musk, attaijiri kuma mu’assanin kamfanin motar Tesla ya ce zai sauka daga mukamin shugaban Twitter idan ya samu wani ’mai wauta da zai karbi aiki’.

Musk ya bayyana hakan ne da safiyar yau Laraba 21 ga watan Disamba, ya rubuta hakan ne a shafinsa na Twitter.

Idan baku manta ba, Musk ya sayi Twitter a shekarar nan, ya kuma bayyana yin wasu sauye-sauye a kamfanin.

Musk ya fadi abin da zai sa ya sauka daga mukamin shugaban Twitter
Zan Yi Murabus a Matsayin Shugaban Twitter da Zarar Na Samu ‘Ba Hamagen’ Magaji, in Ji Elon Musk | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa, zai ci gaba da kula da fannin tirken tushen manhajar kamfanin idan ya samu wanda zai maye gurbinsa.

Kara karanta wannan

Bude 'Border': Atiku ya fadi abin da zai yiwa iyakokin kasar nan idan ya gaji Buhari a 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Zan yi murabus daga CEO da zarar na samu ba hamagen da zai karbi aikin! Bayan haka, zan koma shugabantar tawagar kula da tirken manhajar.”

Yin haka ne daidai a gare ka, martanin Dan Ives ga Elon Musk

Da yake martani ga maganar Musk, babban daraktan kamfanin Wedbush Securities, Dan Ives ya bayyana cewa, ajiye mukamin shugaba ga Musk shine abu mafi dacewa a gareshi, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

A cewarsa:

“Musk ya ce zai yi murabus daga mukamin CEO idan ya samu magaji. Daga karshe dai ya dauki hanya mai kyau domin kawo karshen kunan da masu hannun jari a Tesla ke ji.”

An kada kuri’a, Musk zai sauka a shugabancin Twitter

Attajirin ya yi alkawarin ya yi alkawarin amfani da sakamakon zaben da ya sanya a Twitter, inda kashi 57.5% na mutum miliyan 17.5 da suka kada kuri’a suka ce ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

A zaben, cewa ya yi ranar Litinin:

“Shin ya kamata na yi murabus a matsayin shugaban Twitter? Zan yi amfani da sakamakon da wannan zaben.”

Dama dai Elon Musk na amfani da shafin Twitter wajen yanke shawari, a baya ya yi kuri’a kan yiwuwar dawo da asusun tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump kan manhajar.

Wadannan maganganu dai na zuwa ne bayan da Musk ya sauka daga matsayin wanda yafi kowa kudi a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel