An Harbe Mutum 1, Wasu da Dama Kuma Sun Jikkata a Gangamin Kamfen PDP a Jihar Edo
- Jam’iyyar PDP a jihar Edo ta bayyana shiga jimami yayin da aka kashe wani mutum a wurin taron gangaminta na mazabar sanata
- Wannan lamari ya kai ga wasu mutane da yawa sun samu raunuka, kuma an tattara su zuwa asibiti don yi musu jinya
- Rahoton da muka samo ya bayyana yadda daraktan kamfen na yankin ya yi bayanin gaskiyar abin da ya faru a wurin kamfen
Jihar Edo - Jam’iyyar PDP a jihar Edo ta dage gangamin kamfen dinta har sai baba ta gani biyo bayan kare-jini-biri-jini a wurin wani kamfen a jiya Larana 18 ga watan Janairu.
An ruwaito cewa, mutum daya aka kashe a yayin rikicin, yayin da mutane da yawa suka tsira da raunuka yayin da ake gangami a yankun Ewu na karamar hukumar Esan ta tsakiya a jihar.
Majiya daga yankin ta shaidawa jaridar PM News cewa, wadanda suka samu raunukan yanzu haka suna karbar kulawar likita a a wani asibitin da ba a bayyana ba.
Daraktan kamfen PDP na karamar hukumar, Anselm Ojezua ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana yadda lamarin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya faru
Ya yi karin haske a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis cewa, tuni an kai batun gaban hukumar ‘yan sanda don yin bincike, Platinum Post ta ruwaito.
Ojezua ya kara da cewa, jam’iyyar ta yanke dage taron gangaminta da kacauniyar siyasa saboda faruwa lamarin har sai ‘yan sanda sun fitar da rahoton bincikensu.
A cewarsa, sakamakon gangamin na gunduma ta 1 da ta 5 a mazabar sanatan ya kai ya
Ya kuma bayyana cewa, an samu tsaiko ne a wurin gangamin na kamfen lokacin da aka ji karar harbin bindiga na tashi daga nesa, har ta kai ga aka tattaka mutane a turmutsutsu.
Akwai Yiwuwar Gwamna Makinde Ba Zai Halarci Taron Gangamin Atiku Ba a Jiharsa
A wani labarin kuma, ana dar-dar din cewa, gwamnan jihar Oyo ba zai halarci taron gangamin PDP da Atiku ya shirya a jiharsa ba.
Wannan na zuwa ne kasancewar akwai 'yar tsama tsakanin dan takarar na shugaban kasa a PDP da gwamnan PDP mai ci.
Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Atiku da wasu gwamnonin PDP biyar da ake kira G-5 masu adawa da shugabancin PDP.
Asali: Legit.ng