Ta Karewa Atiku, Jiga-Jigan Siyasa a Jiharsu Abokin Takararsa Sun Koma APC

Ta Karewa Atiku, Jiga-Jigan Siyasa a Jiharsu Abokin Takararsa Sun Koma APC

  • Jam’iyyar PDP ta yi babban rashin mambobinta a jihar Delta, ciki har da Hon Daniel Reyenieju gabanin zaben 2023
  • Reyenieju ya kasance mamban majalisar wakilai ta kasa a mazabar Warru ya sauya sheka zuwa APC a ranar 16 ga watan Janairu
  • Sauran wadanda suka sauya shekan sun hada da tsohon mamban majalisar dokokin jihar, Hon Tonye Timi da wani tsohon hadimin gwamna Okowa, Michael Akpobire

Jihar Delta – Tsohon mamban majalisar wakilai ta kasa, Hon. Daniel Reyenieju ya bayyana ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa ta APC a jihar Delta.

Reyenieju, wanda ya wakilci mazabar Warri a majalisar kasa har sau uku ya bayyana a hukumance cewa shi ba dan PDP bane daga ranar Litinin 16 ga watan Janairu, kana ya bayyana shiga APC.

Atiku ya yi rashi, jiga-jigan PDP sun koma APC
Ta Karewa Atiku, Jiga-Jigan Siyasa a Jiharsu Abokin Takararsa Sun Koma APC | Hoto: Joel-Onowakpo Thomas
Asali: Facebook

Dalilin da yasa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Kara karanta wannan

Babban Mai Daukar Nauyin APC da Dubban Mabiyansa Sun Bar Tafiyar Tinubu, Sun Koma PDP

A cikin takardar barinsa PDP, tsohon dan majalisar ya bayyana cewa, ya bar PDP ne saboda rashin tabuka komai a jihar Delta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce duba da wannan, ya ce ba zai ci gaba da zama a jam’iyyar ba, ya sauya sheka zuwa APC mai mulkin kasa.

A cewar rahoton Nigerian Tribune, Reyenieju ya yi addu’ar Allah ya dafa masa a harkokinsa na siyasa da ya kuma kawo dauki ga gwamnati a jihar Delta.

Legit.ng ta tattaro cewa, dan majalisar ya samu tarba daga jiga-jigan APC a jihar a wani gagarumin biki da aka yi.

Da yake magana a wurin taron, Reyenieju ya yi alkawarin tallata APC da tare da tabbatar da ta yi nasara a zabukan da ke tafe nan kusa.

Ya ce PDP ba gidan zai ci gaba da zama bane saboda mambobinta sun saba daga manufofin jam’iyyar, ya kuma ce ya shiga APC ne don kubutar da jihar Delta daga rugujewa.

Kara karanta wannan

Kayan marmari ya rube: Mambobin NNPP miliyan 2.8 sun koma PDP, sun ba Kwankwaso shawara

Sauran wadanda suka bar PDP, suka koma APC

Baya ga Reyenieju, akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka bayyana ficewa daga jam’iyyar ta PDP tare da yin mubaya’a ga tsagin Tinubu, Naija News ta ruwaito.

Daga cikinsu akwai tsohon dan majalisar dokokin jihar, Hon. Tonye Timi da kuma tsohon hadimin gwamna Okowa, Kwamared Micheal Akpobire.

Dan takarar sanata na jam’iyyar APC a mazabar Delta ta Kudu, Hon. Joel-Onowakpo Thomas ne ya karbi sabbin mambobin.

Ya bayyana su a matsayin mutanen da ke kwarewa a siyasa da rayuwa, kuma za su kawo ci gaba a APC.

A irin wannan yanayin ne dan takarar shugaban kasa a NNPP, Kwankwaso ya rasa mambobin jam'iyyar sama da miliyan 2.8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.