Shaidanun Aljanu ke Rike da Akalar Aurenmu: Matar Aure Mai Neman Saki a Kotu

Shaidanun Aljanu ke Rike da Akalar Aurenmu: Matar Aure Mai Neman Saki a Kotu

  • Wata mata mai siyar da kayayyaki ta gurfana gaban wata kotun Mapo Grade A a Ibadan da rokon raba aurenta da mijinta Adewale saboda ya ce shaidanun aljanu ne ke dawainiyar da auren
  • Kamar yadda matar ta bayyana, tayi barin juna biyu a 2005 daga nan bata kara ko batan wata ba, hakan yasa mijinta ya kai ta wurin malaminsa har tayi wasu abubuwa
  • Daga nan ne Olagunju ya ce mata ta gaggauta barin gidan saboda akwai bakaken aljanu, tun daga sannan ita kadai take rayuwa

Wata 'yar kasuwa, Sarata Olagunju, a ranar Alhamis shaidawa wata kotun Mapo Grade A a Ibadan da ta raba aurensu da mijinta, Adewale ya ce shaidanun aljanu ne ke dawainiya da auren.

Kotun raba aure
Shaidanun Aljanu ke Rike da Akalar Aurenmu: Matar Aure Mai Neman Saki a Kotu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A hatsaniyar da tayi da mijinta, Olagunju ta ce:

Kara karanta wannan

Babu Ruwanmu da NEPA: Budurwa Ta Nunawa Duniya Katafaren Gidan Iyayenta a Bidiyo, Jama'a Sun Shiga Mamaki

"Ya ce min akwai shaidanun aljanu a gidan aurenmu kuma dole in gaggauta bari.
"Nayi barin juna a 2005 inda tun daga lokacin ban kara samun juna biyu ba. Olagunju ya kai ni wurin malaminsa wanda ya umarce ni da in yi wasu irin abubuwa kuma na musu biyayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Olagunju ya ce min in bar gidan saboda akwai wasu bakaken kuma shaidanun aljanu a gidan.
"Tun daga lokacin ni kadai nake rayuwa."

A baya, Olagunju, wanda ke sana'ar jari bola, ya bayyana dalilin da yasa ya shigar da karar saboda rashin haihuwa.

Mai karar ya ce bai biya kudin auren da ya dace ba kafin ta dawo wurinsa, Daily Nigerian ta rahoto.

Yayin sauraron shari'ar, shugabar kotun, S.M Akintayo ya tsaya kan cewa ba za a raba auren da ke tsakanin Sarata da Olagunju ba saboda ba a biya kudin aure ba.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Kama Jarumin da ya Caka wa Makwabcinsa Wuka a Kirji kan N1,000

Yayin kawo wani bangare na doka don karfafa shari'arta, Mrs Akintayo ta ta tsaya kan cewa Sarata da Olagunju basa zama tare.

Sai dai, ta amince da bukatar Olagunju da ya shigarwa kotu na dakatar da wacce ake kara daga hantara, tsangwama, cin zarafi ko shiga rayuwar wanda ke karar.

Makauniya mai kitso da daura kallabi ta birge jama'a

A wani labari na daban, wata yarinya mai makanta ta ba jama'a mamaki bayan ta nuna kwarewarta a fannin kitso a bidiyo.

Ba a nan ta tsaya ba, yarinyar ta kware a rangada daurin kallabi wanda ya matukar dacewa da zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel