Na Dawa Muslunci, Jarumin Fim a Najeriya Ya Zama Musulmi

Na Dawa Muslunci, Jarumin Fim a Najeriya Ya Zama Musulmi

  • Jrumin fina-finai a Najeriya ya bayyana shiga addinin Islama yayin da ya bayyana asalin yadda aka haife shi
  • Abdurrasheed Bello ya ce dama shi a Muslunci aka haife shi, kawai ya bi addinin mahaifiyarsa ce wacce ba Musulma ba
  • Ya zanta da wata jarida, inda ya bayyana mata kadan daga dalilan da suka sa bai addinin Islama ba

Najeriya - Fitaccen marubucin fina-finai da wakoki a Najeriya, AbdulRasheed Bello wanda aka fi sani da JJC Skillz ya bayyana dawowa addinin Islama, addinan da mahaifinsa ke kai.

Jarumin na fina-finan Nollywood kuma mijin jaruma Funke Akindele ya bayyana dawowarsa Islama ne a shafinsa na Instagram.

Hakazalika, ya yi tattaunawa da wata jaridar yanar gizo ta addinin Islama a ranar Alhamis don bayyana aniyarsa.

Abdulrasheed Bello ya dawo addinin Islama
Da Sake Dawowa Muslunci, Jarumin Fim a Najeriya Ya Fita Daga Islama, Ya Sake Dawowa | Hoto: jjcskillz
Asali: Instagram

JJC Skillz ya ce, dama an haife shi a matsayin Musulmi, kuma danginsa Muslmai ne masu suna sallah, amma ya bi addinin mahaifiyarsa wacce ba Musulma ba.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Yi Mani Alkawarin N10m Domin Yi Wa Bukola Saraki Sharri – ‘Dan Fashi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Allah ya ganar dani hanya

A cewarsa:

“Na kasance cikin bata amma yanzu na fahimta Ya Allah, ina rokon yafiyarka da lafiya a nan duniya da lahira.
“Ya Allah, ya hijabance rauni na ka yaye mani bakin ciki, kuma ka kare ni ta baya da ta gaba na sannan ta dama na da hagu na da kuma sama na, kuma ina neman kariyarka kada na shagala da duniya."

Addinin mahaiyata na bi

Da yake zantawa da Muslims News, mawakin ya bayyana cewa, Allah ya nufa zai rabauta ya karbi addinin Islama.

A cewarsa:

“An haife Muslunci - Sunana Abdulrasheed. Mahaifina, Bello Musulmi ne amma mahaifiyata Kirista ce.
"A baya can da ina zuwa Islamiyah amma abin da nake tunawa kawai shine yadda ake duka na. Suna tsoratar damu da wuta don haka, ban taba yi ba.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Mai Nakasu Bayan Ta Rabu Da Attajirin Saurayinta

“Nufin Allah ne yasa na dawo addinin Islama. Na godewa Allah da ya tsiratar da rayuwata.
“Ina matukar farin ciki da na gane addinin Islama saboda ya bani zaman lafiya. Ya bani taswirar rayuwa da manufa. Da gaske da ina cikin bata, amma yanzu na gane.”

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

A wani labarin, Mercy Aigbe ta ce shugar da Musulmai mata ke yi na ba ta sha'awa, don haka take sanya irin tufafin.

Ta bayyana cewa, za ta iya karbar addinin Islama anan gaba, domin addinin na ba ta annashuwa da jin dadi.

Da ma wannan jaruma tana auren wani Musulmi a matsayin mata ta biyu, don haka tana da alaka da addinin Islama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel