Shugaba Mai Mutunci Zan Marawa Baya a Zaben 2023, Gwamna Wike Ya Magantu Game da Dan Takara

Shugaba Mai Mutunci Zan Marawa Baya a Zaben 2023, Gwamna Wike Ya Magantu Game da Dan Takara

  • Yayin da ake ci gaba da jiran martani da batun wanda gwamnonin G-5 za su zaba, gwamna Wike ya fadi alamun nasa dan takarar
  • Ya ce zai zabi shugaba ne mai mutunci da karamci sabanin shugaban da haka kawai zai ba shi kuri'unsa
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnonin G-5 da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsu ta PDP

Jihar Ribas - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas kuma mamban tawagar da ke adawa da Atiku, G5 ya ce nan kusa zai bayyana wanda zai zaba a zaben 2023 a matsayin shugaban kasa.

A cewarsa, abokan shawarinsa a siyasa za su marawa dan takara mai gaskiya da nagarta ne kuma ba za su kitsa wata yarjejeniya boyayya ba, Tribune Online ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a Rumuji-Odegwe yayin kaddamar da kamfen PDP na jiharsa a karamar hukumar Emohua a ranar Laraba 18 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Wike ya magantu game da irin shugaban da zai zaba
Shugaba Mai Mutunci Zan Marawa Baya a Zaben 2023, Gwamna Wike Ya Magantu Game da Dan Takara | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

Yayin da jiga-jigan siyasar jihar suka shaida masa cewa sun gaji da jira, amma za su ci gaba da jira, Wike ya ce zai yi magana nan ba da dadewa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ya ce zai yi maganin dukkan wadanda ke ganin jihar Ribas ba komai bace kuma ba ta da tasiri ga siyasar bana.

Ya kara da cewa:

“Idan kuka yi wasu damu, za mu yi wasa daku. Idan suka yi wasa da mu, za muyi wasa dasu. Yanzu kam ya isa.”

Ga irin dan takarar da zan marawa baya a 2023

Da yake game da shugaban da ya kamata mutanensa su zaba, TheCable ta naqalto shi yana cewa:

“Wannan zaben shugaban kasan batu ne na mutunci, batu ne ga cika alkawari, batu ne na tambayar ‘waye kai’. Dole mu san waye kai. Idan za muyi wani abu da kai, za ka iya cika alkawari? Idan ba za ka cika ba, sai wata rana.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Wike Ya Yi Sabuwar Magana Kan Wanda Zai Goyi Baya a 2023

Gwamna Wike da daya daga cikin gwamnonin biyar da ke nuna adawa da shugabancin jam’iyyar PDP, suna son a tsige Ayu Iyorchia daga shugabancin jam’iyyar.

A baya dama daya daga cikin gwamnonin G-5 ya ce bai da burin zaben Atiku, kuma ba zai kakaba ma mutanensa zabinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.