Wani Mutum Ya Harbi Direba Da Bindiga Kan Wurin Fakin A Abuja

Wani Mutum Ya Harbi Direba Da Bindiga Kan Wurin Fakin A Abuja

  • Wani abin tashin hankali ya faru a Abuja yayin da wani mutum ya harbi wani direban Uber
  • Wani shaidan gani da ido ya ce hayaniya ce ta shiga tsakanin mutum da ya yi harbi da direban kan wurin fakin
  • Rundunar yan sandan Abuja ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma ce an kai direban asibiti yana samun sauki, an kuma bazama neman wanda ya yi harbin

FCT Abuja - An kwantar da wani direban Uber a asibiti bayan wani dan bindiga ya harbe shi a Gimbiya Street, a Garki, birnin tarayya Abuja, rahoton The Punch.

Wani mazaunin garin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce mutane suna shakatawa misalin karfe 10 na dare sai suka ji mutane biyu na hayaniya.

Abuja
Wani Mutum Ya Harbi Direba Da Bindiga Kan Wurin Fakin A Abuja. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Doka a hannu: Kiristoci a jihar Arewa sun fusata, sun kone ofishin 'yan sanda saboda abu 1

Majiyar ta ce:

"Kamar yadda ka sani, an saba hiran dare a nan, za ka ga mutane suna jayayya kan wurin fakin din mota.
"Amma, mutane sun yi mamaki lokacin da suka ji karar harbin bindiga bayan hayaniya tsakanin direban Uber da wani mutum mai bindiga. Hasali, babu wanda ya san yana dauke da bindiga. An ce an kai direban asibiti; muna fatan ya rayu."

Ba fashi da makami bane, Martanin yan sandan Abuja

Mai magana da yawun yan sandan Abuja, Josephine Adeh, cikin sanarwar da ta fitar ta ce lamarin ba fashi bane.

Ta ce:

"Binciken farko da yan sanda suka yi ya nuna a ranar Litinin, 16 ga watan Janairu, an yi rikici tsakanin wani direban Uber da wani da ba a san sunansa ba kan wurin fakin kan Gimbiya Street, Garki.
"Rikicin ya janyo dambe hakan yasa mutumin mai bindigan ya harbi dayan (direban uber) ya kuma tsare.

Kara karanta wannan

Tsantsar fikira: Bidiyon yadda matashi ya kera motar da ba a taba ganin irinta ba, ya tuka ta

"Da samun rahoton mara dadi, jami'an yan sandan Garki sun isa wurin sun ceto direban Uber da aka raunata suka kai asibiti mafi kusa inda ya ke samun sauki."

Adeh ta ce kwamishinan yan sandan Abuja, Sadiq Abubakar ya umurci a yi cikakken bincike da binciko wanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164