Kudin Bogi Na Yawo, Mai POS Ya Ba Wani N1,000, Ya Gano Matsala Bayan Kwanaki

Kudin Bogi Na Yawo, Mai POS Ya Ba Wani N1,000, Ya Gano Matsala Bayan Kwanaki

  • Wani dan Najeriya ya shiga mamaki yayin da aka ba shi kudin bogi da sunan sabbin Naira da CBN ta buga
  • Ya yada hoton kudaden kuda biyu, ya nemi mutane su gane bambancin da ke tsakaninsu don kaucewa zamba
  • Jama'ar kafar sada zumunta sun yi martani, sun bayyana shakku kan yadda ci gaba da karbar sabbin kudi

Najeriya - 'Yan damfara sun kirkiri kudaden bogi masu kama da sabbin Naira da ke yawo a yanzu a Najeriya.

Wani dan jarida a Najeriya, Ali Ahmed Geidam ya bayyana yadda wani mai sana'ar hada-hadar kudi ta POS ya bashi kudin bogi.

Hakazalika, ya gargadi 'yan Najeriya da su ma su kula, domin kuwa akwai kudaden bogi da yawa da ke yawo a kasar nan fiye da kima.

An cuci wani da kudin bogi da sunan sabbin Naira
Kudin Bogi Na Yawo, Mai POS Ya Ba Wani N1,000, Ya Gano Matsala Bayan Kwanaki | Hoto: Ali Ahmed Geidam
Asali: Facebook

Geidam ya yada hoton da ke nuna kudin gaske da na bogi, inda ya yi kira da mutane da su fahimci bambancin da ke tsananinsu.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jikin kudin gaske, akwai wani tambari mai launin gwal amma babu a jikin N1000 na bogi da ya yada.

Da yake bayyana alhinin abin da ya faru dashi, Geidam ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"An damfare ni kwanakin baya a wurin mai POS. Sai jiya na gane, lokacin da aka ki karbar N1000 na bogi da na bayar. Ku duba ta yadda za ku gane na karya. Kuma a yi hattara."

Tun bayan fitar da sabbin kudi 'yan Najeriya ke zaman dar-dar game da yadda kudaden bogi ke yawo a kasar.

Kalli hoton:

Martanin jama'ar Facebook

A bangare guda, jama'ar kafar sada zumunta sun bayyana martaninsu game da abin da ya faru da dan jaridan ga kadan daga abin da suke cewa:

Ashiedu Ogboli yace

"Ta yaya za ka tantance wannan idan kana hada-hada da yawa na dubban kudade a gidan mai, kasuwa, kantin masarufi ko wurin masu nama da masu shinkafa?"

Kara karanta wannan

Wannan Abun Kunya Har Ina? Bidiyon Fasto Yana Zage Mambobin Coci Kan Bada sadakar N100 da N20

Mohammed Haruna yace:

"Hmmm! Idan babban yayanmu zai fada wannan tarkon to ya kamata mu maida hankali."

Isah Suleiman Ibrahim yace:

"Allah ya tsare mu daga zalumtar kawunanmu."

Asil Ahmad Grema yace:

"Bai da tambarin gwal a kasa ta hannun hagu."

Babangida Rufa'i Wurno yace:

"Tunani kawai kashe kudi ba tare da rike tsaba ba..."

Har yanzu dai ana ci gaba da kai ruwa rana game da batun sabbin kudi, gwamnan CBN bai tsira daga barazanar kamu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.