Babu Ritayar da Sifeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya Zai yi a 2023, FG ta Magantu

Babu Ritayar da Sifeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya Zai yi a 2023, FG ta Magantu

  • Ministan kula da lamurran 'yan sanda, Mohammed Dingyadi, ya bayyana cewa Usman Baba Alkali ba zai yi ritaya a wannan shekarar ba kamar yadda ake ta hasashe
  • Ya sanar da cewa, a dokar aikin 'yan sanda ta 2020 da ya sani Sifeta Janar din zai kwashe shekaru hudu a kan karagarsa
  • Ya sanar da hakan ne ga manema labaran gidan gwamnati a yau bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta tarayya

FCT, Abuja - Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ba zai yi ritaya ba ana tsaka da shirin zaben 2023. A maimakon hakan, tuni an bada wasikar tsawaita masa wa'adin mulkinsa.

IGP Alkali Baba
Babu Ritayar da Sifeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya Zai yi a 2023, FG ta Magantu. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ministan kula da lamurran 'yan sanda, Mohammed Dingyadi, ya bayyana hakan ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwar tarayya da aka yi na farko a 2023.

Kara karanta wannan

Karin bayani Gwamnan CBN ya shiga tasku, 'yan sanda sun mamaye gidansa da dare

Ana ta hasashen a cikin kwanakin nan cewa shugaban 'yan sandan Najeriyan zai cika shekaru 60 a ranar 1 ga watan Maris din 2023, hakan zai sa yayi murabus kamar yadda dokar aikin gwamnti ta tanadar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, sai dai, yayin martani ga tambayar da manema labaran gidan gwamnati suka yi kan cewa IGP zai yi ritaya kamar yadda ake tsammani, Dingyadi yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ban sanda inda kuka samo naku lissafin ba amma daga tanadin dokar 'yan sanda ta 2020, Sifeta Janar ya kamata yayi shekaru hudu ne kuma shugaban kasa tuni ya bada wasika kan hakan.
"Toh batun IG zai tafi yayin wannan lokacin zaben ma bai taso ba."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Alkali Baba wanda a bayan DIG ne zuwa matsayin babban 'dan sandan Najeriya a ranar 6 ga watan Afirilun 2021.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Babbar Kotun Tarayya Tayi wa Gwamnan CBN Kiran Gaggawa, Tana so Ya Bayyana Gabanta

Majalisar kula da harkokin 'yan sandan ta tabbatar da shi matsayin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya a watan Yunin 2021.

Ana ta cece-kuce da damuwa kan ritayar sifeta janar din, DIG uku na 'yan sanda, AIG masu yawa da kwamishinonin 'yan sanda har da wasu 'yan sanda 290 a farkon wata ukun 2023.

Dingyadi ya kara da bayyana cewa majalisar zartarwar ta amincewa da bukatar kafa makarantun 'yan sanda a Najeriya wanda yace zai samar da goyon bayan shari'a ga makarantun horarwar da ke fadin kasar nan kuma ba gina sabbi ba.

Ya kara da tabbatar da cewa, rashawa a tsakanin jami'an 'yan sandan Najeriya ya ragu ba kadan ba.

FG ta magantu kan batun dagewa ko fasa zabe

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya tace babu gudu balle ja da baya kan batun dagewa ko fasa zaben Najeriya na shekarar 2023.

hakan ya biyo bayan sanarwan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ne kan batun dage zabe sakamakon farmakin da ake kaiwa ofisoshinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel