Babbar Kotun Tarayya ta Abuja Tayi wa Gwamnan CBN Kiran Gaggawa

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja Tayi wa Gwamnan CBN Kiran Gaggawa

  • Wata kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bukaci Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya da ya gaggauta bayyana a gabanta ranar Laraba
  • An maka Gwamnan bankin ne gaban kotu kan wasu kudi har $53 miliyan da ya rike na kamfanin Linas ya ki biyansu bayan an sahhale masa ya biya
  • Kotun tace zai bayyana gamsasshen dalilin da zai sa ba za a tasa keyarsa zuwa gidan yari ba kan wannan take hakkin da yayi na shekaru

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yi kiran gaggawa ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, kan ya bayyana a gabanta ranar Laraba a kan hukuncin $53 miliyan na biyan bashi da ya fito daga Paris Club.

Gwamnan Bankin CBN
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja Tayi wa Gwamnan CBN Kiran Gaggawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai shari'a Inyang Ekwo a wata bukatar da ya fitar a ranar 20 ga watan Oktoban 2022, ya umarci Emefiele da ya bayyana gaban kotun a ranar 18 ga Janairun 2023, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista, Lauyoyi, Sun ja Kunne kan Amfani da DSS wajen cafke Gwamnan CBN

Umarnin ya biya bayan bukatar da SAN Joe Agi ya shigar kan Linas International Ltd, ministan kudi da CBN ta lauyoyinsa, Isaac Ekpa da Chinonso Obasi inda ya ke bukatar a yi umarni ga Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya da ya kama Emefiele.

Bayan kama shi, ya mika shi kotu tare da lauyoyinsa: Damian Dodo, Audu Anuga, dukkan manyan lauyoyin Najeriya da Ginika Ezeoke, Jessica Iyole, Abdullahi Afolayan da Olayemi Afolayan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Karar ta samo tushe ne kan zargin hukuncin $70 miliyan kan Linas kan ayyukan lauyoyi a biyan bashin Paris Club, wanda Emefiele ya saki $17 miliyan inda ya bar bashin $53 miliyan.

Kotun a ranar 23 ga watan Janairun 2020, ta yanke hukuncin cewa, dole Emefiele ya bayyana a gaban kotun tare da bayyana dalilin da zai sa ba a za atura shi gidan yari ba kan kin biyan wannan kudin duk da yana da damar biyansu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Babban Banki Ya Koma Bakin Aiki, CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa

DSS ta zagaye babban bankin Najeriya

A wani labari na daban, jami'an tsaron farin kaya na DSS sun mamaye farfajiyar babban bankin najeriya da ke da hedkwata a Abuja.

Wannan na faruwa ne bayan dawowar Gwamna Bankin, Godwin Emefiele daga hutun shekara tare da komawa kan aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng