Yan Jarida Na Arcewa Daga BBC: Akalla Mutum 9 Sun Yi Murabus Kawo Litinin

Yan Jarida Na Arcewa Daga BBC: Akalla Mutum 9 Sun Yi Murabus Kawo Litinin

  • Sabanin labarin zazzaga da akafi samu da kamfanoni keyi, wannan karon ma'aikatan da kansu suka ajiye ayyukansu
  • Kimanin yan jarida goma sun ajiye ayyukansu a kafar jaridar Hausa mafi dadewa a tarihi
  • Majiyoyi sun bayyana cewa yan jaridar gaba dayansu sun koma sabuwar tashar TRT Hausa

Akalla yan jaridar tara sun yi murabus daga sashen Hausa na BBC cikin wata guda, irin abin da bai taba faruwa a tarihin gidan jaridar ba.

Yan jaridan da suka yi murabus sun hada da manyan yan jaridar biyu, na kafafen sada zumunta uku, na bidiyo biyu, dss, rahoton DailyTrust.

Rahoton ya kara da cewa da farko mutum biyar suka yi murabus a watan Disamba; sannan a ranar Litnin na makon nan wasu karin hudu sukayi murabus.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Yadda Malami da Matarsa Suka Mutu a Kokarin Ceto Dansu Daga Nutsewa a Ruwa

bbchausa
Yan Jarida Na Arcewa Daga BBC: Akalla Mutum 9 Sun Yi Murabus Kawo Litinin
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiya ta bayyana cewa murabus dinsu ke da wuya, sun garzaya sabuwar tashar rediyo da talabijin na kasar Turkiyya TRT dake Istanbul.

Majiyar ta ce:

"Wannan abu bai taba faruwa ba a tarihin BBC Hausa. Yan Najeriya tara na BBC sun koma sabon TRT Hausa bayan gwamnatin kasar Turkiyya ta shirya bude TRT Afrika: Hausa, Swahili, Faransa da Turanci."

DailyTrust ta ruwaito majiyar da cewa Nasidi Adamu Yahaya, ya yi murabus daga matsayinsa kuma zai zama saboda shugaban sashen Hausa a TRT.

Sauran yan jaridan da suka yi murabus sun hada da Halima Umar Saleh da Ishaq Khalid.

Daya daga cikin yan jaridan da suka yi murabus, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa kawai tashar TRT ce ta ja ra'ayinsu saboda suna son yada labarun alkhairi a Afrika.

Kara karanta wannan

Maganar Hadin Kan Bola Tinubu da Wata Babbar Jam’iyyar Siyasa Na Daf da Tabbata

Yace:

"TRT na son sauya yadda ake yada labarai. Sauran kafafen yada labaran kasashen waje sun kasance masu wallafa labarai kan yunwa, yaki da labaru mara dadi game da Afrika."
"Ba wai ba zamu rika kawo labarai kan Boko Haram, yan bindiga da sauran su bane, amma akwai labarun abubuwan alheri dake faruwa. Akwai labaran taimakon da ake yiwa wadanda rikiicin Boko Haram ya shafa."

Dan jaridan ya kara da cewa BBC Hausa bata taba fuskantar irin wannan ba, ko ranan Litinin wasu sun yi murabus.

Yace:

"Wasu zasu fita (daga BBC) yau (Litinin) yayinda wasu zasuyi murabus nan da yan kwanaki. Mu biyar muka tafi a Disamba, BBC Hausa na da yan jarida sama da 40, amma yanzu, kashi 1 cikin 3 sun tafi."

An fasawa Amarya Ido ana shagalin bikinta a Kano, Ango yace ba zai yarda ba

BBC ta ruwaito labarin amaryar da aka fasawa ido ana tsaka da shagalin daurin aurenta.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Wannan shagalin aure ya gudana ne a unguwar Kwalajawa dake jihar Kano.

Angon Hamza Bala ya bayyana cewa shi dai ba zai yarda ba kuma wajibi ne a kwatowa Amaryarsa hakkinta.

Asali: Legit.ng

Tags:
BBC
Online view pixel