Hukumar Kwastam Ta Yi Nasarar Kame Tufafin Sojoji, ’Yan Sanda da Kwayoyi Masu Yawa

Hukumar Kwastam Ta Yi Nasarar Kame Tufafin Sojoji, ’Yan Sanda da Kwayoyi Masu Yawa

  • Hukumar kwastam a Najeriya ta yi nasarar kame wasu kayayyaki masu ban mamaki da aka shigo dasu kasar
  • An shigo da kakin soja da na 'yan sanda Najeriya daidai lokacin da ake shirin yin babban zaben 2023
  • An kuma kama wasu miyagun kwayoyi da aka shigo dasu daga kasashen Indiya da Pakistan kamar yadda aka bayyana

Jihar Legas - Hukumar Kwastam a Najeriya ta yi nasarar kame wasu tufafin sojoji da na ‘yan sanda da aka shigo dasu kasar.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, na kama kayan ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas, kamar yadda BBC ta ruwaito.

A cewar rahoto, an yi fasa-kwabrin kayan ne daga kasar Afrika ta Kudu kuma sun shigo ne ba bisa ka’ida ba.

Kwastam sun kama kayan sojoji da aka shigo dasu Najeriya
Hukumar Kwastam Ta Yi Nasarar Kame Tufafin Sojoji, ’Yan Sanda da Kwayoyi Masu Yawa | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Bello Kaniyal Dangaladima ne ya bayyana hakan ga kafar labaran, inda ya bayyana dalla-dalla kayayyakin da aka kwato.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Wike Ya Yi Sabuwar Magana Kan Wanda Zai Goyi Baya a 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

A cewarsa, daga kayayyakin da aka kwato sun hada da riguna, hulunan kwano na sojoji da kakin ‘yan sanda irin na Najeriya.

Baya ga kayan na jami’an tsaro, an kama wasu miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol na masu darajar Naira biliyan 37.

Ana kyautata zaton an shigo da miyagun kwayoyin ne daga kasar Pakistan da Indiya, kuma ana ci gaba da bincike a kai.

Wannan babban kamu dai nasara ce ga kwastam, kuma ya zo daidai lokacin da kasar nan ke shirin babban zaben 2023.

Fusatattun Kiristoci a Neja Sun Yi Aikin Dana-Sani, Sun Kone Ofishin Yanki Na ’Yan Sanda

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sandan Najeriya ta gamu da halin daukar doka a hannu daga wasu kiristoci a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya a yau Talata 17 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, fusatattun mata da matasa sun kone ofishin 'yan sanda kurmus bayan da 'yan bindiga suka kone wani babban fastonsu kurmus kuma ya sheke kiyama.

An tattaro cewa, 'yan sandan sun zo ne domin ba mutanen kariya, amma lamarin ya rikide zuwa tashin hankali, 'yan sanda sun harbi mutum daya daga cikinsu, wanda hakan ya sa suka tada hankali a wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.