Matasa Sun Halaka Basarake Har Gida, Gwamnati Ta Kakaba Dokar Kulle a Neja

Matasa Sun Halaka Basarake Har Gida, Gwamnati Ta Kakaba Dokar Kulle a Neja

  • Rikicin matasa a Lambata karamar hukumar Gurara a jihar Neja ya yi sanadin mutuwar Dagacin garin, Mohammed Abdulsafur
  • Gwamnatin Neja ta hannun SSG ta sanar da sanya dokar zaman gida a yankin har sai baba ta gani, ta yi Allah wadai da kisan
  • Bayanai sun nuna cewa Basaraken ya cika ne sakamakon raunukan da matasan suka ji masa yayin da suka shiga gidansa

Niger - Magajin Garin Lambata da ke ƙaramar hukumar Gurara a jihar Neja, Mohammed Abdulsafur, ya rasa rayuwarsa sakamkon wani rikici da ya barke tsakanin matasa da yammacin jiya Asabar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Abdulsafur ya riga mu gidan gaskiya ne sakamakon raunukan da ya matasan suka masa yayin harin.

Taswirar jihar Neja.
Matasa Sun Halaka Barake Har Gida, Gwamnati Ta Kakaba Dokar Kulle a Neja Hoto: thenationonlinenh
Asali: UGC

Har yanzun ba'a gano dalilin kai masa harin ba amma bayanai sun nuna cewa matasa ne suka shiga har gidan Basaraken suka kai masa farmaki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ta tono badakala, ya ce likitoci 199 cikin 280 a jiharsa ma'aikatan bogi ne

Gwamnatin jihar Neja karkashin gwamna Abubakar Sani Bello ta tabbatar da mutuwar magajin garin kuma ta kakaba dokar zaman gida har sai baba ta gani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da Sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya fitar yace dokar zata fara aiki daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safiyar kowace rana.

Ya kara da bayanin cewa wannan matakin da gwamnati ta dauka zai taimaka wa hukumomin tsaro su shawo kan lamarin, tsare rayukan al'umma da kuma dawo da doka da oda.

"Gwamnati ta yi Allah wadai da da rikicin da ya barke da kuma take doka wanda ya faru a garin Lambata." inji sanarwan.

Mutane su baiwa jami'an tsaro hadin kai - Gwamnati

Bugu da kari, gwamnatin jihar Neja ta yi kira ga mazauna yankin da su bai wa hukumomin tsaro hadin kai a kokarinsu na dawo da zaman lafiya a garin Lambata.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi Yayin Da Najeriya Da Ukraine Ke Shirin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Ta Noma

Gwamnatin ta kuma roki hukumomin tsaro su shiga ko ina a yankin don tabbatar da dokar zaman gidan na aiki yadda ya kamata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma Wasu miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malamin Addini a Jihar Ekiti

'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani babban Malamin Majami'ar Katoli, Rabaran Fada Michael Olofinlade, a Oye jihar Ekiti.

An cewa maharan sun tasa Malamin Cocin ne yayin da yake hanyar komawa gida daga Ado-Ekiti, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262