Atiku Ne Zai Gaji Buhari a Zaben Bana, Wani Malamin Addini Ya Yi Hasashe
- Wani fitaccen malamin addinin kirista ta ce Atiku ne zai gaji Buhari a zaben 2023 da ke tafe nan kusa
- Ya ce Peter Obi ya kama addu'a kawai, domin zai riga rana faduwa a ranar da za a yi zaben shugaban kasa
- Atiku Abubakar da Bola Tinubu ne kan gaba a jerin 'yan takarar da suka tsaya a zaben 2023 mai zuwa nan da wata guda
Jihar Kwara - Fitaccen malamin addini mai hangehange a jihar Kwara, Christopher Olabisi sabanin abin da ake tsammani, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe zaben shugaban kasa na bana.
Ya kuma yi kira ga da a dukufa da addu'o'i a gabanin zaben da ke tafe nan kusa, rahoton jaridar Tribune Online.
Olabisi, wanda kuma shine mai kula da cocin Christ Apostolic Church (CAC) na Redemption Mountain da ke kan hanyar Ilofa a yankin Omu Aran a jihar Kwara, ya ce ya hango matsaloli gabanin da bayan zaben na bana.
Ya kamata a yi ta addu'a a kasar nan, akwai matsaloli masu zuwa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, idan kowa ya dukufa da yin addu'o'i, to tabbas duk wata matsala da ya hango za ta kau da izinin Allah.
Ya kara da cewa, za a samu matsaloli da ke da alaka da doka, amma tabbas Atiku ne zai ci zabe kuma zai mulki Najeriya yadda ya kamata.
A kalamansa:
"Ba Atiku ne mai ceto ba amma tabbas zai cike gurbi tsakanin shugaba na gaskiya da zai bayansa.
"Zai gina tubali mai inganci ga wanda zai gaje shi da kowa zai sani a matsayin shugaban kasan da yake da hangen nesa."
Malamin ya kuma bayyana cewa, shugaban kasan da zai zo bayan Atiku zai ciyar da Najeriya gaba fiye da yadda shugabannin baya suka yi.
PDP za ta dawo jihar Kwara, Saraki zai samu babban matsayi, inji malami
Hakazalika, ya ce, zaben 2023 zai zama hanyar da dawo da mulkin PDP a jihar Kwara cikin yanayi mai ban mamaki, inda ya kara da cewa
"Jam'iyyar PDP za ta karbe gidan gwamnatin Kwara."
Da aka tambaye shi game da makomar Sanata Bukola Saraki da 'yan tawagarsa, ya ce tsohon sanatan sam bai da wani abin da ya kamata ya ji tsoronsa ya yanzu.
Ya hangowa Saraki cewa, zai samu matsayi a mulkin Atiku duk da kuwa bai samu wata kujerar takara da ya tsaya ba, The Informant ta tattaro.
Daga karshe ya hango makomar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, ya ce zai dungura a zaben, don haka ya yi ta addu'ar kada ciwon zuciya ta kama shi.
Koma dai yaya ne, Buhari ya ce kada 'yan Najeriya su bari su zabi wanda zai wargaza kasar nan, domin ya sha wahalar gyara ta.
Asali: Legit.ng