Zaben 2023: Shugaban Kasa Mai 'Rowa' Najeriya Ke Bukata, In Ji Peter Obi

Zaben 2023: Shugaban Kasa Mai 'Rowa' Najeriya Ke Bukata, In Ji Peter Obi

  • Mr Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ya ce Najeriya na bukatar shugaban kasa marowaci
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce ya gode wa Allah ba a kira shi mai almubazaranci ba ko mai bannatar da kudaden al'umma
  • Obi ya ce aikin shugabancin kasa ba wuri ne na samun bashin yin murabus ba, wuri ne na aikin gina kasa da hadin kan kasa

Anambra - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, a ranar Talata ya ce kujerar shugabancin Najeriya ba wurin cin bashin yin murabus bane, ya ce kasar na bukatar shugaba mai 'rowa' a yanzu.

Obi ya ce ba zai bawa kowa hakuri ba saboda makonsa, ya kara da cewa shine mafi karancin shekaru kuma mafi cancanta a cikin manyan yan takarar hudu, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu Ko Atiku: An Tona Sunan Dan Takarar da Kwankwaso da Peter Obi Suke Wa Aiki a Zaben 2023

Peter Obi
Shugaban Kasa Mai 'Rowa' Najeriya Ke Bukata, In Ji Peter Obi. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan za a iya tunawa Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP duk sun taba kiran Obi, marowaci, Nigerian Tribune ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar da ya yi da sarakunan Anambra a gidan gwamnati, Awka, a matsayin kamfen dinsa na zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu.

Na ji dadin cewa marowaci aka kira ni, ba mai bannatar da kudin al'umma ba - Obi

Ya ce:

"Wannan ba zancen lokacin wani bane, ana batu ne na cancanta, mutane kamar mu za mu iya cewa lokacin mu kuma a duba mu.
"Aikin shugaban kasa ba wurin samun bashin murabus bane amma hadin kan kasa da gina kasa ake magana.
"Sun ce ni mai mako ne, sai na ce ba su ce min mai almubazaranci ba ko na bannatar da kudin al'umma kawai dai ni mai mako ne kuma na fada maka aikin shugaban kasa a yanzu na bukatar mai mako."

Kara karanta wannan

Abin Duniya Bai Dameni Ba, Ku Rike Amana: Shugaba Buhari

Bayan taronsa da masu ruwa da tsaki a Awak, dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour zai tafi Onitsha, inda ake fatan zai gana da magoya bayansa da suka taru a can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel